Yanzu-yanzu: Amurka ta kashe babban kwamandan Sojin Iran, Qassim Sulaiman

Yanzu-yanzu: Amurka ta kashe babban kwamandan Sojin Iran, Qassim Sulaiman

Kasar Amurka ta kai mumunan harin jirgin sama domin hallaka babban kwamandan kasar Iran, Qassem Soleimaini da kwamandan rundunar Kata’ib Hezbollah na Iraqi, Abu Mahdi Muhandis.

Hedkwatan hukumar Sojin Amurka, Pentagon, ta tabbatar da hakan a jawabin da ta saki cewa lallai harin Amurka ya kashe kwamandan rundunar Al-Quds na Iran, Qassem Soleimani, a filin jirgin saman Baghdad dake Iraq.

Kata’ib Hezbollah kungiya ce da kasar Iran ke daukan nauyi a Iraqi kuma Amurka ta hallaka mambobinta akalla 15 a makon da ya gabata.

Hedkwatar Sojin Amurkan ta ce shugaban kasa, Donald Trump, ne ya bada umurnin kashe kwamandojin biyu dake shirin kai hari ofishin jakadancin Amurka a Iraqi.

Jawabin yace: "Bisa ga umurnin shugaban kasa, hukumar Sojin Amurka ta dauka tsattsaurin mataki wajen yake jami'an Amurka dake waje ta hanyar kisan shugaban rundunar Sojin kwato AlQuds, Qassem Soleimani."

"Soleimani na cikin masu shirye-shiryen kaiwa yan diflomasiyyan Amurka hari a Iraqi."

"Shine ummul haba'isin kisan daruruwan yan Amurka da Sojin gammaya da kuma jikkatan dubunnai."

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, ya bayyana cewa kasar Iran da abokanta za su mayar da martani kan ta'addancin Amurka na kisan kwamandan Sojin Iran kuma shugaban rundunar kwato Al-Quds, Qassem Soleimani.

Rouhani ya bayyana hakan ne da safiyar Juma'a, 3 ga watan Junairu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel