Yanzu-yanzu: An cafke wanda ya tsara fashin bankin da 'yan sanda suka dakile Abuja (Hoto)
- 'Yan sanda sun kama wani Ernest Ewim da ake ganin shine ya tsara fashin bankin da aka shirya a Mpape a Abuja
- Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a wani bankin zamani a ranar Asabar 28 ga watan Disamba a Mpape da ke Abuja amma 'yan sanda suka taka musu birki
- Mai magana da yawun 'yan sandan Abuja, DSP Ajugunri Manzah ya ce an kama Ewim ne a ranar Laraba 1 ga watan Janairun 2020
Jami'an 'yan sanda sun kama wani Ernest Ewim mai shekaru 29 a duniya da ake ganin shine ya shirya fashin bankin da wasu 'yan binidiga suka ka yi yunkurin yi a wani banki da ke Mpape a Abuja amma ba ayi nasara ba.
The Nation ta ruwaito cewa an yi yunkurin fashin bankin ne a unguwar Mpape da ke Abuja a ranar Asabar 28 ga watan Disamban 2019.
Legit.ng ta gano cewa sanarwar ta mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Abuja, DSP Ajugunri Manzah ya fitar a ranar Alhamis 2 ga watan Janairu ta tabbatar da kama Ewim.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Soja mafi tsufa a Najeriya ya rasu yana da shekara 101 (Hotuna)

Asali: Twitter
Sanawarwar ta ce: "Sakamakon binciken da ake gudanarwa kan yunkurin fashin bankin da ake yi a Mpape, 'yan sandan sashi yaki da masu fashi da makami sun kama wani Ernest Ewim dan shekaru 29 da ke cikin gungun 'yan fashin da ake nema."
A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya taka muhimmiyar rawa a fashin bankin da 'yan sanda suka dakile kuma jami'an yan sanda sun kama shi ne a mabuyarsa da ke Kamtampe1 a ranar Laraba 1 ga watan Janairu kimanin karfe 4 na yamma.
"A halin yanzu jimlan wadanda aka kama bisa zargi da hannu a fashin ya kai 5 :- Ernest Ewim dan shekaru 29, Larry Ehizo dan shekara 30, Princewill Obinna dan shekara 24, Timothy Joe dan shekara 21 da Elijah David dan shekara 19."
Sanarwar ya kara da cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin ta na cigaba da kiyaye lafiya da dukiyoyin mazauna Abuja. Za kuma a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu indan an kammala bincike.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng