Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Miji ya yiwa surukarsa gunduwa-gunduwa

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Miji ya yiwa surukarsa gunduwa-gunduwa

- Wani mutum ya kashe sirikarshi da adda inda daga bisani ya sha guba ya sheka lahira

- Mutumin ya rabu da matarshi ne inda ta koma gidansu, lamarin da ya bata mishi rai kuma ya fusata shi

- Bayan da matar ta hango mijinta da addar, ta tsere tare da barin mahaifiyarta wacce ke fama da matsanancin ciwon kafa

Wani mutum ya kashe sirikarshi. Jaridar The Nation ta gano cewa lamarin ya faru ne a titin Arubayi dake Warri, jihar Delta a cikin sa’o’i kalilan da suke rage na sabuwar shekara.

An gano cewa mutumin daga bisani ya sha guba inda ya mutu har lahira.

Ganau ba jiyau ba, wanda ya tattauna da jaridar The Nation ya ce, mutumin ya je gidan sirikan ne da adda da nufin ya hari matarsa wacce suka yi fada. Amma kuma sai matar tashi ta tsere bayan da ta ga mijin nata.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, ma’auratan sun rabu inda matar ta koma gidansu. Amma kuma mijin sam baya farin ciki da wannan rabuwar, shi ne ya yanke hukuncin harar matar tashi amma sai aka yi rashin sa’a ya koma kan mahaifiyarta.

Jaridar The Nation ta gano cewa, mata da mijin suna da yara biyu da Ubangiji ya albarkacesu da su.

KU KARANTA: Budewa da Bismillah: Amal Umar za ta zama jarumar Kannywood ta farko da za ta fara aure a wannan shekarar

Wani matukin adaidaita sahu da ya ga yadda lamarin ya faru, ya ce: “Ta gudu amma mahaifiyarta ta kasa guduwa saboda ciwon kafa da take fama dashi. Mutumin sai ya sassari sirikar tashi da addar inda a take ta mutu.

“Makwabta suma tserewa suka yi saboda sun tsorata da lamarin. Amma sai mutumin ya sha guba inda ya sheka lahira.”

Majiya daga rundunar ‘yan sandan yankin ta tabbatar da aukuwar lamarin. Ta ce gawawwakin na ma’adanar gawawwaki dake babban asibitin Warri.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adeyinke Adeleke ya tabbatar da cewa mutumin ya kashe kanshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel