Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Kwara ta rusa gidansu Bukola Saraki
Gwamnatin jihar Kwara ta rusa gidan mahaifin tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, dake Ilori, babbar birnin jihar.
Legit Hausa ta samu labarin cewa jami'an rusau sun dira gidan ne cikin dare bayan jami'an tsaro sun wargaza yan zanga-zangan da suka mamaye gidan.
Gwamnatin jihar ta rusa gidan ne cikin daren gudun rikici da masoyan Bukoa Saraki da suka kafa suka tsare a gidan.
Kalli bidiyon:
Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana dalilinta na karbe wasu filaye kwanakin baya a Garin Ilorin na Iyalin Marigayi Sanata Olusola Saraki.
Shugaban hukumar da ke kula da harkar filaye a jihar Kwara, Mista Ibrahim Salman, ya bayyana cewa ainihi filin na ginin sakatariya ne.
Ibrahim Salman wanda shi ne Darekta Janar na hukumar ya ce har da wurin ajiye motocin ma’aikata ya kamata a gina a wadannan filayen.
“Ainihi an karbe filin a shekarun 1970 ne bayan an danne hakkin al’umma, kuma ya kamata ace an gina sashen sakatariyar Kwara ne a wurin.”
“An fara aikin sakatariyar jihar har an soma gini kafin ayi watsi da aikin. A shekarun 1980 kuma aka canza tsarin aikin da za ayi a kan filayen.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng