Aisha Buhari ta karrama jaririn da aka fara haifa a Najeriya a sabuwar shekarar 2020

Aisha Buhari ta karrama jaririn da aka fara haifa a Najeriya a sabuwar shekarar 2020

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta karrama jaririn da aka fara haihuwa na farko a sabuwar shekarar 2020, a karamin asibitin dake garin Gwagwa, na babban birnin tarayya Abuja.

Premium Times ta ruwaito Aisha Buhari ta samu wakilcin uwargidar kaakakin majalisar wakilai ne, Hajiya Salamatu Gbajabiamila, inda ta taya iyayen jaririn da aka haifa da misali karfe 12:00 na daren 1 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Jagoran yan bindiga ya bayyana yadda haduwarsa da kwamishinan Yansanda a daji ta kasance

Aisha Buhari ta karrama jaririn da aka fara haifa a Najeriya a sabuwar shekarar 2020

Aisha Buhari ta karrama jaririn da aka fara haifa a Najeriya a sabuwar shekarar 2020
Source: Facebook

Iyayen jaririn, Malam Sani Ardo da Malam Hauwa sun bayyana farin cikinsu da samun wannan karramawa, inda suka rada ma jaririn nasu suna Muhammad Sani. Baya ga jariri Muhammad Sani, duk sauran jariran da aka haifa a sabuwar shekarar a asibitin sun samu kyaututtuka daban daban.

Shugaban karamar hukumar AMAC ta babban birnin tarayya Abuja, Adamu Candido ya bayyana farin cikinsa da wannan lamari, sa’annan ya mika godiyarsa ga uwargidar shugaban kasar da wakiliyarta, ya kara da daukan alkawarin tabbatar da daukan nauyin kulawar yaron har a yaye shi.

Ita ma a nata jawabin, ma’aikatar kula da harkokin mata ta Najeriya da ta shirya ziyarar ta bayyana godiyarta ga uwargidar shugaban kasa ta bakin babbar sakatariyar ma’aikatar Ifeoma Anagbogu saboda kulawar da take baiwa gajiyayyu da marasa galihu.

Daga karshe, Aisha Buhari ta nanata muhimmancin daukan kwararan matakan kulawa da jarirai ga iyayensu mata, musamman abin da ya shafi shayar dasu nono, kais u allurar riga kafi da kuma sauran kulawar da suke bukata bayan haihuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel