Yanzu-yanzu: Soja mafi tsufa a Najeriya ya rasu yana da shekara 101 (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Soja mafi tsufa a Najeriya ya rasu yana da shekara 101 (Hotuna)

A jiya ne ranar 31 ga watan Disamba 2019, Aduku ya rigamu gidan gaskiya. Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya taba mika kambun girmamawa ga Aduku wanda rundunar sojin Najeriya ta bashi idan ba zamu manta ba.

A safiyar yau ne daya daga cikin 'yan uwansa ya sanar da rasuwarsa ta Whatsapp a dandalin yada labarai na hedkwatar tsaro.

An haifesa ne a 1918 a Abejukolo-Ife, a karamar hukumar Omaha ta jihar Kogi. Aduku ya shiga aikin soja ne a shekarar 1945.

Tsohon ya sanar da jaridar The Punch a wata hira da yayi da ita, cewa har yanzu yana da karfi hatta a kan gado duk da wannan shekarun nashi.

Tsohon sojan ya bayyana cewa bai taba tunanin shiga rundunar soji ba amma daga baya sai tunaninsa ya sauya. Wani matashi ne ya zane sarkin kauyensu a wancan lokacin

DUBA WANNAN: Ban taba ganin shugaba mai bin tsarin demokradiyya kamar Buhari ba - Yahaya Bello

"A ranar ina dawowa daga gona ne naga wani matashi da na girma yana zane sarkin kauyenmu na wannan lokacin," Aduku ya ce.

"Sunan mutumin Salikawa kuma soja ne da ya zane sarkin kauyenmu, saboda bai daukar masa jakarsa zauwa gidan sa dake mil goma daga inda na gansu ba. A lokacin da aka kai karar Salikawa zuwa gaban babban sojin yankin, sai ya shawarci sarki da ya dinga biyayya ga sojoji." cewar Aduku.

"Abun ya matukar bata min rai kuma a take na yanke shawarar shiga aikin soja ta yadda zan dawo kauyenmu don in zane Salikawa saboda tozarta sarkinmu da yayi." Ya sanar da Punch a yayin tattaunawa da jaridar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel