Dan Allah ku dinga sanya mu a hanya idan munyi abinda ba daidai ba - Sanata Ahmad Lawan ya roki 'yan Najeriya

Dan Allah ku dinga sanya mu a hanya idan munyi abinda ba daidai ba - Sanata Ahmad Lawan ya roki 'yan Najeriya

- Shugaban majalisar dattijai yayi kira ga 'yan Najeriya dasu kasance masu kira garesu a yayin da suka ga sun kauce

- Ya ce zasu kafa majalisa wacce zata aje banbancin jam'iyyar siyasa don ganin habakar Najeriya

- Kowanne dan Najeriya na da burin ganin habakar arzikin kasar nan da kuma zaman lafiya ba tare da duban jam'iyyar siyasa ba

Shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan, ya bukaci 'yan Najeriya dasu dinga ba 'yan majalisar shawara a duk Inda suka kauce.

Shugaban majalisar dattijan ya yi wannan kiran ne a lokacin da aka karramashi tare da Abubakar Aliyu, karamin ministan aiyuka da gidaje , a Damaturu jihar Yobe a ranar Asabar.

Ya ce: "Inaso inyi amfani da wannan damar wajen kira ga 'yan Najetiya dasu cigaba da goyon bayanmu a majalisar dattijai. Ku bamu shawara kuma ku nuna mana Inda muka kauce ko zamu kauce."

KU KARANTA: Tonon asiri: Ango ya kunna bidiyon amaryarshi a wajen shagalin bikinsu, inda aka ganta tana lalata da wani kato a daki

Lawan yayi alkawarin kafa majalisa wacce take duban bukatar 'yan Najeriya da farko kafin kowa.

"Da kaina na dau alkawarin kafa majalisa ta 'yan Najeriya kuma don Najeriya. Majalisa wacce jam'iyya bata da ta cewa a kan abinda ake yi.

"Kowanne dan Najeriya na da burin ganin habakar tattalin arziki mai dorewa tare da zaman lafiya, ba tare da duban jam'iyyar siyasa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel