Kano: Dalilin da yasa aka dakatar da dokar haramcin mace da namiji hawa adaidaita daya

Kano: Dalilin da yasa aka dakatar da dokar haramcin mace da namiji hawa adaidaita daya

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana dakatar da dokar hana maza da mata shiga adaidaita sahu guda a jihar. Amma kuma tace har yanzu wannan dokar na nan daram, kawai dakatar da tabbatar da ita akayi a shekarar 2020.

A ranar Litinin ne aka ruwaito yadda gwamnatin jihar Kano ta dakatar da dokar wacce zata fara aiki a gobe, daya ga watan Janairu 2020.

Kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Harun Ibn-Sina ne ya tabbatar da wannan cigaban a taron manema labarai da aka yi a yau Talata a babbar hedkwatar Hisbah din.

Kamar yadda ya sanar, wannan ba sabuwar doka bace tunda ta kasance tun a 2005. Ya ce ba dage dokar aka yi ba, dakatar da tabbatar da ita aka yi.

Jaridar Solacebase dake Kano ta rawaito cewa majiya mai karfi daga cikin gwamnati ta sanar da ita, a daren ranar Litinin, cewa gwamna Ganduje ya dakatar da kaddamar da dokar ne saboda rudanin da ta fara kawowa tun yanzu tare da tabbatar da ganin cewa kaddamar dokar bai haifar da rikici ba.

DUBA WANNNAN: Na karanta Qur'ani sau 6, Islam addini ne na zaman lafiya - Babban Fasto, Apostle Suleiman

Tun a makon jiyan Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin jihar Kano ta haramtawa mutane mabanbantan jinsi hawa adaidaita sahu daya a fadin jihar daga watan Janairu 2020.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin rufe bikin IVC da aka yi karo na 77 wanda kungiyar musulmai ta kasa ta shirya. Hakan ya faru ne jami'ar Bayero dake Kano.

Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya ce gwamnatin jihar ta shirya tsaf wajen jaddada hukunce-hukunce addinin Islama.

Kamar yadda aka sani, an fara gabatar da adaidaita sahu ne a jihar Kano tun zamanin mulki Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a matsayin sufuri ga mata zalla.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel