Buratai ya karawa jami'an Soji 5 girma kan jaruntar da suka nuna wajen yakan Boko Haram

Buratai ya karawa jami'an Soji 5 girma kan jaruntar da suka nuna wajen yakan Boko Haram

Hukumar Sojin Najeriya karkashin jagorancin babban hafsa, Laftana Janar Tukur Buratai, ta karrama jaruman Soji biyar kan bajinta da jarintar da suka nuna wajen yakan yan ta'addan Arewa maso gabashin Najeriya.

Hakazalika an karrama yan kungiyar kato da gora biyu da suka taimakawa Sojoji bisa ga bajintarsu.

Hukumar Soji ta yabawa jaruman Sojojin ne ta hanyar kara musu girma na musamman.

An sanar da karin girman ne a taron wasanni da hukumar Sojojin Najeriya ta shirya na yankin Afrika ta yamma da ya gudana ranar Litinin a garin Gwoza, kudancin jihar Borno.

DUBA NAN: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban bankin cigabar Afrika AfDB

Babban hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa wannan taron na wasanni na da tarihi a gidan Soja kuma akan gudanar ne domin murnar karshen shekara.

Ya ce an gudanar taron na wannan shekarar a garin Gwoza ne domin nuna cewa Sojoji sun ci karfin Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Ya jinjinawa Sojojin kan nasarorin da suka samu a fadin tarayya kuma ya tabbatar musu da cewa za'a bunkasa lamuran jin dadinsu a shekarar 2020.

A bangaren gwamnati kuma, gwamnan jihar Bonro, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bada N200,000 ga kowanne cikin jaruman Sojojin da yan kato da goran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel