'Yan fashi sun kai wa Khadi hari, sunyi awon gaba da direbansa

'Yan fashi sun kai wa Khadi hari, sunyi awon gaba da direbansa

- Wasu da ake zargi 'yan fashi ne sun harbi Khadi na kotun daukaka kara na shari'a na jihar Kogi a hannunsa

- An harbi Bala Muhammed ne a hanyar Okene-Lokoja a ranar Lahadi 29 ga watan Disamba a hanyarsa ta zuwa wurin wasan kwallon kwando a Ajanah

- Wadanda ake zargin 'yan fashin sun kuma sace direban mai shari'ar yayin harin

Wasu 'yan bindiga da ke ake zargi 'yan fashi ne a ranar Lahadi, 29 ga watan Disamba sun harbi Khadi na kotun daukaka kara na jihar Kogi, Bala Muhammad.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun kai wa khadin hari ne a hanyar Okene zuwa Lokoja a ranar Lahadi.

An gano cewa Khadin yana hanyarsa ne zuwa kallon wasan gasar kwallon kwando da ake gudanarwa a Ajanah inda 'yan bindigan suka sace direbansa yayin harin.

Wadansu shaidu da suka ce abin ya faru a gabansu sun ce 'yan bindigan sun tsayar da motar Khadin ne kafin Itakpe sannan suka harbe shi a hannunsa.

DUBA WANNAN: Yadda wata amarya ta daure fuska a hoton auren ta ya dauki hankalin mutane

Wadanda ake zargi 'yan fashin ne sun kuma kwace wa Khadin kayayakin da ya ke dauke da su sannan suka yi awon gaba da direbansa.

An garzaya da shi zuwa babban asibitin Okene don yi masa magani kana daga bisani aka mayar da shi Lokoja.

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku kun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabanin hukumomin tsaro a fadarsa ta Aso Rock a Abuja.

An gudanar da taron ne a ranar Litinin 30 ga watan Disamba inda rahotanni suka ce shugaban hasfin sojojin kasa na Najeriya, Tukur Buratai bai hallarci taron ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel