'Yan Hisbah sun kama wani dan sanda a Otal da mata uku a daki

'Yan Hisbah sun kama wani dan sanda a Otal da mata uku a daki

Hukumar Hisbah a jihar Zamfara ta sanar da cewa ta kama wani jami'in dan sanda tare da wasu mata uku suna aikata masha'a a wani Otal dake birnin Gusau.

Shugaban hukumar Hisbah a jihar, Dakta Atiku Zawuyya, shine wanda ya sanar da hakan ranar Litinin yayin holin masu laifin da dakarun Hisbah suka kama suna aikata laifuka da suka ci karo da tsarin Musulunci.

Ya ce sun kama dan sandan, wanda ke aiki da babban ofishin 'yan sanda na Gusau, yana aikata abubuwan da suka saba wa Shari'ar Musulunci a dakin wani Otal.

Dakta Zawuyya ya bayyana cewa binciken da hukumar Hisbah ta fara gudanar wa ya gano cewar daya daga cikin matan ta zo ne daga jihar Kaduna yayin da sauran biyun 'yan uwan juna ne da suka fito daga dangi daya a jihar Zamfara.

'Yan Hisbah sun kama wani dan sanda a Otal da mata uku a daki

Jami'an Hisbah
Source: Twitter

Shugaban ya kara da cewa hukumar Hisbah ta sha jan kunnen mahukuntan Otal din a kan saba ka'idoji da dokokin gudanar da kasuwanci irin nasu a jihar, amma suka yi burus da gargadin.

DUBA WANNAN: Jerin kasashen duniya da Buhari ya ziyarta a shekarar 2019

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa dakarun hukumar Hisba sun kama manajan Otal din.

Dakta Zawuyya ya ce zasu gurfanar da jami'in dan sandan a gaban kotu da zarar sun kammala bincike a kansa da kuma matan da aka samu shi tare da shi a dakin Otal din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel