'Yan sanda sun tarwatsa taron 'yan Shi'a a Sokoto

'Yan sanda sun tarwatsa taron 'yan Shi'a a Sokoto

'Yan sanda a ranar Juma'a a jihar Sokoto sun tarwatsa dandazon 'yan kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da suka taru domin yin tattaki a jihar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Lamarin da ya faru a shataletalen Danbuwa da ke hanyar Airport Road a ranar Juma'a ya gudana ne cikin tsari da bin dokokin aiki a cewar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, ASP Sadiq Abubakar.

Ya ce babu wanda ya rasa ransa a kishiyar abinda wasu kafafen yadda labarai na intanet ke yadawa. Ya kuma ce ba su yi amfani da harsashi na ainihi ba yayin tarwatsa 'yan shi'an.

DUBA WANNAN: Kaico: Yadda Boko Haram suka kashe amarya da kawayenta a hanyarsu ta zuwa daurin aure

Abubakar ya ce, "Binciken da muka yi da farko ya nuna cewa wasu gungun mutane da ake zargin 'yan Shi'a ne sun fito a kan tsohon Airport Road da niyyar yin tattaki.

"Bayan tabbatar da abinda suka yi niyyar aikatawa, jami'an tsaro sun tarwatsa su ba tare da amfani da karfi mai tsanani ba yayin da su kuma 'yan kungiyar su kai ta jifar 'yan sandan da motarsu da duwatsu da niyyar tayar da tarzoma.

"Sai dai an tabbatar da doka da oda cikin kankanin lokaci bayan da jami'an tsaro na hadin gwiwa suka kawo dauki.

"Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto tana kira ga al'umma su cigaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da tsoro ko fargaba ba saboda rundunar ta baza jami'an tsaro a wuraren da suka dace domin kare afkuwar haka a gaba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel