Azumi sau biyu a kowanne mako na kara tsawon rai da kuma kariya daga cututtuka - Cewar Masana a Amurka

Azumi sau biyu a kowanne mako na kara tsawon rai da kuma kariya daga cututtuka - Cewar Masana a Amurka

- A kasar Amurka ne wasu ma'abota bincike suka gano amfanin yin azumi sau biyu a mako

- Binciken ya nuna cewa, yin azumi ko kame baki na zama garkuwa ko kuma riga-kafin wasu cutuka

- Masana sun tabbatar da cewa azumin na tsaftace jini da daidaita sinadarin Insulin wanda hakan ke da matukar amfani ga masu ciwon sukari

A Amurka ne masana suka gano cewa azumi sau biyu a kowanne mako na kara tsawon rai da kariya daga cututtuka.

Masana kimiyya a Amurka sun bayyana cewa, sakamakon wani bincike da suka gudanar, an gano azumi a kowanne mako ko kuma kame baki daga barin cin abinci na wasu awanni a rana na kara tsawon rayuwa tare da zama riga-kafin cututtuka da dama.

Masanan sun ce, azumi sau biyu a kowanne mako na kara tsawon rai da riga-kafi ga garkuwar jiki.

An buga sakamakon wannan binciken ne a mujallar Likitanci ta New England. Ta bayyana cewa cin abinci a cikin awanni 16 zuwa 18 na kowacce rana na kara tsawon rai, rage karfin harbawar jini da riga-kafin cututtuka da dama.

KU KARANTA: Wata sabuwa: An kirkiro sabuwar manhajar waya ta yiwa mata kishiya

Rahoton ya kara da bayyana cewa, yin azumi sau biyu kacal a mako na iya maganin cutukan zuciya, rage kiba da ciwon sukari. A saboda haka ne ake shawartar mutane da su yi kasance masu kame bakinsu a kalla sau biyu a kowanne mako.

An gudanar da binciken ne a kan mutane da dabbobi kuma an gano cewa azumi na daidaita sarrafuwar abinci da gudanar jini a jikin dan Adam, sannan yana sabunta lafiya.

Hakazalika, yana magance karancin sinadarin insulin wanda hakan abu ne mai kyau ga masu ciwon sukari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel