Yadda mijina yayi kokarin yanke kai na dana 'ya'yanmu domin yin asiri damu

Yadda mijina yayi kokarin yanke kai na dana 'ya'yanmu domin yin asiri damu

- Wata matar aure mai suna Abidat Ademola ta tunkari wata kotun gargajiya da bukatar a raba auren ta na shekaru 12

- Ta zargi mijinta da fada wa kungiyar asiri da yunkurin kasheta da 'ya'yanta don amfani da sassan jikinsu don yin kudi

- Alkalin kotun ya yanke igiyar auren tare da umartar mijin ya rika bata dubu 20 duk wata, duk da mijin yaki halartar kotun

Wata matar aure mai suna Abidat Ademola ta tunkari kotu da bukatar a raba aurenta mai shekaru 12 da mijinta mai suna Isa Ademola. Hakan kuwa ya bijiro ne bayan zargin yunkurin tsafi da ya so yi da sassan jikinta da 'ya'yansu hudu wadanda ya samu nasarar kashesu.

Abidat ta sanar da kotun dake Oja Oba/Mapo da ke Ibadan cewa, asirin mijinta ya tonu ne a lokacin da ya fara yin abubuwan mamaki da bai saba yi ba.

Ta ce, hakan ne yasa ya kasa amsa tambayoyin da tayi mishi. "Maimakon amsa tambayoyina, sai mijina ya tattara kayanshi ya fice daga gidan ba tare da sanin inda ya koma da zama ba. Hakan ya biyo bayan kararshi da na kai gidan iyayenshi," in ji ta.

Abidat wacce ke kuka a lokacin da take bayanin gallazawar da take zargin mijinta da yi mata tare da 'ya'yansu hudu, musamman rashin abinci da bukatun rayuwa.

KU KARANTA Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Mutane 15 sun rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin sama a Kazakhstan

"Ina rokon kotu da ta tilasta wa mijina biyan kudin abincin yarana kuma a hana shi zuwa gidan iyayena da wurin aikina yana ci min mutunci a gaban jama'a," inji ta.

Mijin Abidat bai bayyana a gaban kotun ba duk da sammacin da aka aika masa kafin ranar Juma'a da ta gabata da aka saurari karar.

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun Ademola Odunade, ya raba auren tare da amince wa Abidat ta ci gaba da rike 'ya'yansu hudu, kuma kotun ta umarci Isa Ademola da ya rika aikewa matar da naira dubu 20 kowanne wata domin dawainiyar yaran.

Zai rika aikawa da kudin ne ta hannun kotun kuma ya gargade shi da kada ya sake zuwa gidan matar ko wurin aikinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel