Budurwar da iyayenta suka shafe shekara da shekaru suna nema, an gano ta tana sheke ayarta a shafin Twitter

Budurwar da iyayenta suka shafe shekara da shekaru suna nema, an gano ta tana sheke ayarta a shafin Twitter

- Allah mai karfin mulki da buwaya ne cikin ikonshi yasa aka gano wata budurwa da ta bace tun tana karama

- Dan uwan budurwar ne ya wallafa hotonta tare da bayyana cewa suna neman a shafinsa na tuwita

- Ta bata ne tun tana da shekaru 5 zuwa 6 a duniya bayan rasuwar mahaifinsu

Allah mai iko da yin abinda ya so a lokacin da yaso. An gano wata budurwa wacce tayi shekaru da bacewa ta tuwita.

Kamar yadda dan uwan budurwar ya bayyana, ta bar gida ne tun tana da shekaru biyar kacal a duniya. Ta bata ne tun bayan rasuwar mahaifinsu kuma ita ma tayi batan dabo.

Ya wallafa hotonta a kafar sadar zumuntar zamani kuma ba a dau lokaci mai tsayi ba aka gano inda take.

Kamar yadda ya ce, “Ina bukatar taimakon kowa da kowa. Ina da ‘yar uwa da ta bata a shekaru masu yawa da suka gabata. Tun bayan rasuwar mahaifinmu. Ina tunanin zata yuwu tana nan tare damu. Duk wanda ya gani ya kara wallafawa har mu ganta.

KU KARANTA: Mutane 9 sun mutu, 100 na kwance rai a hannun Allah, bayan sun dirki barasa mai guba

“Ina da shekaru 5 zuwa 6 ne lokacin da muka rabu. Ina da ‘yan uwa ta bangaren iyayena da yawa. Ban san me ke faruwa dani ba, ita dai kawai nake fatan ganowa.”

Babu dadewa kuwa wannan saurayi yayi gam da katar inda aka gano kanwar tashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel