Dasuki ya yi magana a kan cafkesa, ya bayyana abinda ke tsakaninsa da Buhari

Dasuki ya yi magana a kan cafkesa, ya bayyana abinda ke tsakaninsa da Buhari

Tsohon mai bada shawara a fannin tsaro, Sambo Dasuki ya yi bayani a kan garkamesa da gwamnatin tarayya tayi na shekaru hudu. Ya kara da bayyana cewa bashi da wata kulalliya tsakaninsa da kowa.

Dasuki ya bayyana cewa, wannan abun daga Allah ne ba daga kowa. Ya ce babu komai tsakaninsa da shugaba Muhammadu Buhari.

A wata tattaunawar da Dasuki yayi da muryar Amurka, ya yi bayanin cewa ya dena zuwa kotu ne saboda gwamnatin tarayya ta ki sakinsa duk da ya cika dukkan sharuddan belinsa.

Tsohon NSA din ya shiga hannu ne tun a watan Disamba 2015, kuma an gurfanar da shi a gaban kuliya ne a kan almundahanar $2.1bn a yayin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Kudin anyi waddaka dasu ne wajen yakin neman zaben Goodluck Jonathan a 2015.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka hada da sanatoci da kuma tsoffin gwamnoni an gurfanar dasu a gaban kotu sakamakon zarginsu da ake da karbar kudi daga Dasuki yayin kamfen.

DUBA WANNAN: Ganduje ya sake zama gwarzon gwamnonin APC

Da aka tambayesa ko ya kalli tsaresa da aka yi a matsayin mayar da martani a rawar da ya taka a juyin mulkin 1985 wanda ya ture gwamnatin Buhari, Dasuki da yayi shekaru hudu a hannun jami’an tsaron farin kaya ya ce, bai san da wannan nufin ba.

Ya ce tsaresa da aka yi daga Allah ne kuma ba shi da tsokaci ga gwamnati a kan wannan lamarin.

Dasuki ya ce: “Abinda na sani shine komai da ya faru dani daga Allah ne. Ikon Allah ne kadai ba saka hannun wani ba. Rashin ilimi da yadda da kaddarar Ubangiji ne yasa wasu mutane suke danganta abunda ya faru da ni da wasu mutane. Komai kaddarar Ubangiji ne. Kamar yadda kuka sani, an tsare ni na shekaru hudu amma a yau gani na samu yanci na. Allah kadai ya san abinda zai faru gobe.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel