Kano: Gwamnati ta rufe gidan 'Mayu'

Kano: Gwamnati ta rufe gidan 'Mayu'

- A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kano ta rufe wani gidan 'Mayu' a garin Maloli dake karamar hukumar Dawakin Kudu

- Cibiyar matsafan mallakin wani Yahaya Ali ce, wanda shi ne Ciroman Sarkin Mayu a jihar Kano

- Sun samu majinyatan da aka kwantar a cibiyar masu bukatar tiyata da magunguna cikin gaggawa

Gwamnatin jihar Kano a ranar Laraba ta rufe wani gidan 'Mayu' a garin Maloli dake karamar hukumar Dawakin Kudu ta jihar.

A yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan rufe gidan, sakataren cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu na jihar (PHIMA), Usman Aliyu, ya ce cibiyar matsafan mallakin wani Yahaya Ali ce wanda shi ne Ciroman Sarkin Mayu, wanda yake ikirarin yana warkar da cutukan ta hanyar gargajiya da tsafi.

DUBA WANNAN: Jajiberin Kirsimeti: Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman

Ya ce, a yayin samamen da suka kai, sun samu majinyatan da aka kwantar a cibiyar, masu bukatar aiki da magunguna cikin gaggawa.

Usman wanda kwararren likita ne, ya ce bayan tsananta bincike da ma'aikatan cibiyar suka yi tare da sashin korafi na hukumar yaki da rashawa, an mika majinyata zuwa cibiyoyin lafiyar da suka dace don bincike tare da basu magunguna.

Ya ce, tuni aka mika wadanda ake zargin ga jami'an tsaro don cigaba da bincike tare da daukar matakin shari'a a kansu.

Ya roki jama'a da su guji kai kansu irin wadannan wuraren na masu magungunan gargajiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel