Fada da aljani ba dadi: Barayi sun dawo da kayan da suka sata bayan sunji ruwan asiri

Fada da aljani ba dadi: Barayi sun dawo da kayan da suka sata bayan sunji ruwan asiri

- Barayin da suka kwashewa ‘yan kasuwar Ekiosa kaya bayan da gobara ta kama kasuwar, sun fara mayar musu da kayansu

- Hakan ya biyo bayan kawo shugaban wajen bautar gargajiya na Ayelela da suka yi ya dirka tsinuwa ga barayin

- An mayar musu da kayayyakin da suka hada da buhunan shinkafa, zannuwa, kwalaye da jarkunan man girki, akuyoyi da sauransu

Barayin da suka kwashi kayan ‘yan kasuwar Ekiosa bayan da gobara ta tashi a ranar Lahadi sun mayar musu da kayan da suka sata. Barayin sun mayar da kayan ne bayan da wani malami ya dirka tsinuwa a kan wadanda suka yi satar.

An gano cewa, a ranar Talata da safe ne wasu da ake zargin barayi ne suka dinga mayar da kayan satar zuwa kasuwa da kuma fadar sarkin Benin.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar jihar, Blacky Omoregie, ya tabbatar da rahoton ne a yayin da wakilai daga fadar sarkin Benin, Omo N’Oba N’Edo Uku Akpolokpolo, Oba Ewuare II, suka kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwar.

Ta ce, abubuwa da yawa da suka hada da buhunan shinkafa, zannuwa, kwalaye da jarkunan man girki, akuyoyi da sauransu duk an dawo dasu kasuwar.

KU KARANTA: Asiri ya tonu: An kama mutane 4 sanye da kayan sojoji suna kokarin fashi a banki

“Sun fara dawo da kayan da suka sata sakamakon tsinuwar da aka dirka musu. Sun kara wa ciwon mu gishiri saboda mun tafka asara kuma sun yi mana sata. Ya kamata wadanda suka saka mana gobarar a kama su.”

Daya daga cikin ‘yan kasuwar da abun ya shafa, Gentle Imuetinyan Usoh, wanda ya samu wasu daga cikin kayanshi da aka sace, ya ce zasu kara gayyatar shugaban wajen bautar gargajiya don ya kara tsinuwa ga barayin. Akwai tabbacin sauran zasu fito.

“Tun bayan da aka gayyaci malamin ya yi tsinuwa, mun samu an dawo mana da kayanmu da muka dinga zaton sace su aka yi. Ina da tabbacin cewa za a cigaba da dawo mana da kayayyakinmu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel