Labari mai dadi: Za'a fara kera wasu bangarori na jikin jirgin sama a Najeriya

Labari mai dadi: Za'a fara kera wasu bangarori na jikin jirgin sama a Najeriya

- Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu ya ce Najeriya na da karfin samar da injinan kera sassan jiragen sama

- Ministan ya bayyana hakan ne a kaddamar da wani sassa na hukumar habaka manyan aiyuka ta PRODA da ya yi a Enugu

- Ya jinjinawa hukumar ta yadda take samar da alkalumman rubutu kuma ya bukacesu da zurfafa bincike

Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce Najeriya na da karfin samar da injinan kera sassan jiragen sama .

Onu ya sanar da hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ya je bude wani sassa hukumar habaka manyan aiyuka ta PRODA dake jihar Enugu.

Minsitan ya ce abun murna ne da jin dadi da hukumar ta farfado don taimakawa gwamnatin tarayyar.

Ya ce: “Na ga cigaban da aka samu a wannan hukumar amma akwai bukatar mu kara kokari. Muna son PRODA ta zama babbar cibiya,”

Ministan ya bayyana farin cikinshi ta yadda ya ga injin samar da sassan jiragen sama a hukumar. Ya ce da wannan injinan, hukumar zata iya samar da sassan jiragen da ba zasu yi tsatsa ba ta hanyar amfani da karfen aluminium da sauran karafuna marasa tsatsa.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: China za ta yiwa Qur'ani da Bible kwaskwarima domin suyi dai dai da zamani

Ya kara da kalubalantar hukumar da ta cigaba da bincike a kan yadda ake hada wani nau’in batir don siyarwa.

A fannin samar da alkalumman rubutu kuwa na hukumar, Onu ya ce ya gamsu da yadda suke aikinsu. “Mun fara ganin alkalumman rubutu wadanda PRODA ke kerawa kuma wannan abun jinjinawa ne,” in ji shi.

Ministan ya kara da kalubalantar fannin samar da alkalumman rubutun da su zurfafa bincike don fara kera kowanne irin alkalami har da na zane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel