An yanke wa wani malamin jami'a hukuncin kisa bayan ya zagi Annabi

An yanke wa wani malamin jami'a hukuncin kisa bayan ya zagi Annabi

An yanke wa wani malamin jami’a hukuncin kisa bayan da ya yi batanci ga Annabi Muhammaadu SAW a shafinsa na sada zumunta. Malamin jami’ar mai suna Junaid Hafeez, ya kasance a tsare ne tun bayan da ya wallafa kalaman cin mutunci ga manzon Allah a kafafen sada zumunta a 2013.

Hukumomin Pakistan basu wasa da duk abinda ya shafi batanci ga addini.

A shekarar 2014, an bindige lauyan da ke kare Junaid Rehman, bayan da ya amince zai kare wanda ake zargin da batanci ga fiyayyen halitta.

Junaid ya shafe shekaru a killace shi kadai a gidan mazan bayan karuwar farmakin da wau fursunoi ke kai masa.

A halin yanzu, lauyan da ke kare Junaidu, Asad jamal y ace hukuncin da kotun ta yanke ain takaici ne kuma za su daukaka kara.

DUBA WANNAN: Soyayya: Ahmed Indimi da Zahra Buhari sun yi murnar cikar shekara uku da aure (Hotuna)

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta yi zargin rashin adalci a hukuncin, kungiyar ta bayyana hukuncin a matsayin “mai ban mamaki da ban takaici”.

Tun asali, kasar Pakistan bata amincewa da cin zarafi ko batanci ga addinai ba komai kankantarshi. Turawan mulkin mallaka na Birtaniya ne suka fara yin dokokin a 1869, kuma aka kara fadada su a 1927.

Zuwa yanzu, mutane 40 ne ke garkame a kasar bayan yanke masu hukuncin daurin rai da rai saboda batanci – amma babu wanda aka zartar wa da hukuncin kisa.

Kasashen duniya sun fara sa ido kan dokar batanci a Pakistan bayan da a shekarar 2018 kotun kolin kasar ta soke hukuncin daurin rai da rai da aka yi wa wata mata kirista da ta shafe shekaru 8 a gidan yari, saboda zarginta da akai da zagin manzon Allah.

Sakin matar mai suna Asia Bibi ya haifar da zanga-zanga a fadin Pakistan, lamarin da ya sa Bibi barin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel