Yadda kaza guda 1 ta zama sanadiyyar arzikin wani matashi, inda ta kawo masa shanaye 150

Yadda kaza guda 1 ta zama sanadiyyar arzikin wani matashi, inda ta kawo masa shanaye 150

- Nisa kadan daga babban asibitin Uke dake karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, gonar Hausawa take

- Matashi ne mai shekaru 28 mamallakin gonar mai suna Alhaji Abdullahi Mohammed, Sarkin Hausawan Uke

- Ya bayyana yadda ya mallaki Shanu sama da 150 da Akuyoyi, Tumaki, Agwagi, Kaji da sauransu

Mitoci kadan daga babban asibitin Uke dake karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa ne gonar Hausawa take. Gona ce da take dauke da dabbobi daban-daban da suka hada Shanu, Akuyoyi da Tumakai.

Gonar ta kasance mai jan hankalin manoma. Mamallakinn wannan gonar ba kowa bane face Alhaji Abdullahi Mohammed, Sarkin Hausawan Uke.

Matashin manomin mai shekaru 28 na cike da karfi tare da izza. Yana daukar lokacinshi mai yawa wajen aiki a gonarshi tare da sauran ma’aikatanshi.

Kamar yadda Sarkin Hausawa ya sanar, “Na fara kiwo ne tun ina da shekaru 5 zuwa 7. Wata mata ta bani kiwon kazarta. Da na fara kiwo sai da suka kai 50. Ganin wannan nasarar yasa aka bani kiwon Akuya. Wannan Akuyar sai da ta haifa wasu 30.”

“A lokacin banda wani wayau. Abunda na samu daga kiwon ana min amfanin Sallah dashi. Daga nan ne na gane yadda kiwo ya karbeni. Sai na fara tunanin yadda zan habakashi.

KU KARANTA: Tirkashi: Miji ya yiwa matarshi dukan tsiya saboda ta yanka kazar da ya sayo ta kirsimeti kafin lokaci yayi

“A halin yanzu, mu kan samo maniyyin dabbobi na kasashen ketare masu inganci. Mu kan hada su da irin na nan yankin don samun dabbobi masu nagarta. A halin yanzu akwai Shanu sama da 150, Akuyoyi, Tumaki, Agwagi, Kaji da sauransu. Amma shanu sun fi yawa.”

Alhaji Abddullahi ya tabbatar da cewa a shirye yake don bada taimako ta hanyar koyawa mutane salon kiwonshi. A matsayinshi na wanda ya goge a lamarin kiwo, ya san yadda za a shawo kan tafka asara.

Ya shawarci matasa da su dage wajen neman sana’o’in dogaro da kai don samun mafita a wannan lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel