Tirkashi: Miji ya yiwa matarshi dukan tsiya saboda ta yanka kazar da ya sayo ta kirsimeti kafin lokaci yayi

Tirkashi: Miji ya yiwa matarshi dukan tsiya saboda ta yanka kazar da ya sayo ta kirsimeti kafin lokaci yayi

- Wata mata ta sha mugun duka a hannun mijinta bayan da ta yanka kazar Kirsimati kafin ranar

- Mijin mai shekaru 50 ya yi amfani da guminshi wajen siyan kazar don a yankata a babbar ranar

- A halin yanzu tana gadon asibiti bayan mugun dukan da ya jawo mata raunika da dama

Wata mata na kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, bayan da mijinta yayi mata mugun duka a kan kazar Kirsimati.

An ruwaito cewa, wani mutumin asalin kasar Uganda mai shekaru 50, ya yi wa matarsa mugun duka saboda yanka kazar Kirsimati da tayi ta hada miyarta mai dadin gaske.

Kamar yadda Tok.co.ke suka ruwaito, Kadama yayi amfani da kudinshi don siyan kazar kuma ya umarci matarshi da ta adanata har zuwa ranar Kirsimati.

Mutumin mai shekaru 50 din ya fusata matuka da matarshi bayan da ta sanar dashi ta yanka kazar, kuma ta hada miya mai dan karen dadi kafin babbar ranar.

An gano cewa, ya far wa matar da duka ba ji, ba gani. Ya bugeta da kafa da hannaye wanda hakan ya danganta ta da gadon asibiti.

KU KARANTA: Makarantu ya kamata ka gina ba Masallatai 95 ba - Martanin 'yan Najeriya ga gwamnan jihar Jigawa

Wani jami’in yada labarai mai sun Joseph Gadimba ya bayyana cewa: “Mutumin ya yi wa matarshi bakin duka kuma ya barta cikin mawuyacin hali. A halin yanzu tana karbar agajin likitoci a asibitin Budaka health Centre IV.”

Gadimab ya bayyana cewa, ba a kai karar mutumin gaban ‘yan sanda ba saboda shuwagabannin yankin sun sa mutumin ya biya kudin asibiti.

“Idan matar ta warware, ‘yan uwanta dake Kapyani-Kasasira a yankin Kibuku zasu yi taro da sirikinsu, don gano dalilin wannan cin zarafin ga ‘yarsu,” Joseph Gadimba yayi bayani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel