Kaico! Kasa ta danne kananan yara 3 da ransu a garin Kaduna, sun sheka barzahu

Kaico! Kasa ta danne kananan yara 3 da ransu a garin Kaduna, sun sheka barzahu

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wasu kananan yara su uku sun gamu da ajalinsu a sakamakon ruftawa da kasa ta yi dasu a unguwar Rigasa na karamar hukumar Igabin jahar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yara biyar ne suka gamu da hadarin, amma guda biyu daga cikinsu sun tsallake rijiya da baya, kuma tuni aka garzaya dasu zuwa wani asibiti dake Rigasa domin samun kulawar da ta dace.

KU KARANTA: Miyagu sun halaka Uba da Dansa da ya kawo ziyara daga kasar Amurka a jahar Imo

Wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba da misalin karfe 3 na rana, kuma jama’a sun yi bakin kokarinsu domin ceto sauran yaran uku, amma hakan bai yiwu ba, ana ji ana gani sai dai gawarsu aka tono.

Majiyarmu ta ruwaito yaran su biyar suna kokarin tona rami ne domin su cire wani karfen rodi dake cikin kasa a wani wuri da gwamnati ke gina gada da kwalbati, wannan sanadiyyar ruftawar kasar, inda nan take biyu suka rasu, dayan kuma ya mutu bayan an ceto shi.

Babban limamin Masallacin karshen kwalta, Malam Jamilu ya tabbatar da aukuwar lamarin kamar haka: “Eh, wadanda suka mutu su uku ne, shekarunsu bai wuce daga 12-16 ba, daya daga cikinsu ma yaron makwabcina ne, sunansa Zaharaddeen, ni na musu sallar jana’iza.

“Sun tafi inda ake aikin ginin gawa ne suka fara tonar kasa da nufin ciro wani karfen rodi kamar dai yadda mahaka ke yi, a daidai lokacin nan ne kasa ta rufta da su, ta binnesu da ransu.” Inji shi.

A wani labain kuma, mutane shida ne suka gamu da ajlinsu yayin da kasa ta rufta a kansu a lokacin da suke tsaka da aikin hakar ma’adanan kasa a yankin Zawan cikin karamar hukumar Jos ta kudu a jahar Filato.

Wani shaidan gani da ido, Emmnuel Gyang ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da aka fara samun irin haka a garin, a cewarsa sama da mutane 50 ne suka cikin ramin hakar ma’adanan a lokacin da kasan ya rufta a kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel