Mijina yayi min saki uku saboda na bukaci kwanciya da abokinshi - Mata

Mijina yayi min saki uku saboda na bukaci kwanciya da abokinshi - Mata

Wata mata ‘yar Najeriya da aka bayyana sunanta da Linda ta shiga tsaka mai wuya a jihar Legas, bayan ta roki mijinta ya bari ta kwanta da abokinshi.

Matar ta roki mijin nata ne akan ya bari ta kwanta da abokin nashi ko za ta samu ciki, bayan shafe shekara 8 suna tare babu haihuwa.

A yadda rahoto ya bayyana lamarin ya faru a yankin Agodo Egbe dake Ikotun cikin garin Legas, a inda ma’auratan suke zaune.

Wannan magana da matar ta kaiwa mijin ta sanyata cikin matsala, inda a take a wajen mijin ya nemi ta fita ta bar mishi gidan shi.

Ta ce: “Gani yanzu ina zaune da dangina a Ikorodu, na aikawa da mijina mutane da yawa akan ya yafe mini kan maganar dana yi amma yaki yafe mini.

“Mijina dan kasuwa ne da yake shigo da kaya daga kasashen ketare, amma babban abinda ke ci mana tuwo a kwarya shine rashin haihuwa.

KU KARANTA: Ajali in yayi kira: Dan Najeriyar da ya shekara 45 a kasar Amurka ya gamu da ajalinshi jim kadan da sanya kafar shi a Najeriya

“Mun yi aure shekaru da dama da suka wuce, amma tun wannan lokacin har yanzu bamu samu haihuwa ba.Munje asibiti da wajen masu magungunan gargajiya amma shiru babu labari.”

Ta ce akwai lokacin da likita ya taba gaya mata cewa mijinta yana da karancin ruwan maniyi, haka yasa suka nemi magani, amma bata canja zani ba

Linda ta cigaba: “Na damu matuka akan yadda rayuwata za ta kasance idan ban samu haihuwa ba, mijina ya ce shi ya gaji da shan magunguna ya watsar.

“Ganin wannan abu dake ci mana tuwo a kwarya, yasa na kawo shawarar ya bari na kwanta da abokinshi, amma sai mijina yayi mini wata fahimta daban.”

Wannan dalilin ne yasa mijin yace ta tattare kayanta ta bar mishi gidan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel