Gwamna Badaru zai gina Masallatan juma’a guda 90 a duk fadin jahar Jigawa

Gwamna Badaru zai gina Masallatan juma’a guda 90 a duk fadin jahar Jigawa

Gwamnatin jahar Jigawa a karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ta kammala shirye shiryen fara gina sabbin Masallatai a dukkanin yankunan jahar guda 95 domin amfanin al’umma Musulmai masallata.

Kamfanin dillancin Labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito a ranar Talata, 17 ga watan Disamba ne aka kaddamar da neman kwangilolin ginin Masallatan da suka hada da manyan Masallatan juma’a guda 90, sai kuma na kamsu salawati guda 5.

KU KARANTA: Tabarbarewar tsaro: Gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a jami’ar Filato

Mai magana da yawun ofishin sakataren gwamnatin jahar Jigawa, Alhaji Isma’il Ibrahim ya tabbatar da haka a garin Dutse, inda yace gwamnati za ta gidana wadannan Masallatai ne a mazabu 30 na jahar.

Ibrahim yace kamfanoni da yan kwangila 200 ne suka mika takardun sha’awar neman kwangilolin gina Masallatan, kuma wakilin ofishin bin ka’idar aikin gwamnati na jahar, Ghali Mu’azu ya bayyana cewa zasu tabbatar da gaskiya da adalci wajen tantance kamfanonin.

Shi ma a nasa jawabin, wakilin kamfanonin dake neman kwangilolin, kuma wakilin kamfanin Danfatu and Sons Nigeria Ltd, Malam Yusuf Saminu ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka fara aikin tantancewar.

Sai dai ba wannan bane karo na farko da gwamnatin jahar Jigawa ke yi ma addinin Musulunci hidima ta bangaren ginin Masallaci ba, ko a kwanakin baya sai gwamnatin ta ware naira miliyan 57 domin gina Masallacin mata a jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan siyasar Najeriya, musamman masu burin tsayawa takara ko wacce iri a zaben shekarar 2023 dasu kada su kuskura su sanya shi cikin sabgar siyasarsu.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata, 17 ga watan Disamba yayin da yake tarbar manyan baki da suka kai masa ziyara a fadar Aso Rock Villa domin taya shi murnar cika shekaru 77 a duniya.

Buhari ya nemi yan siyasa masu burin tsayawa takara a zaben 2023 da su kasance sun yi aiki tukuru wajen yakin neman zabe, domin kuwa a wannan karo ba zai sake bari a yi amfani da sunansa wajen tafka magudin zabe ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel