Yaki da rashawa: Ganduje ya samu lambar yabo ta musamman

Yaki da rashawa: Ganduje ya samu lambar yabo ta musamman

Shugaban Fair Play Sports International, Jacob Onu, ya karrama Gwamnan jihar Kani, Abdullahi Ganduje a kan kafa ofisoshin yaki da rashawa a duk kananan hukumomi 44 na jihar don yaki da rashawa.

An mika wannan lambar yabon ne ga gwamnan a jiya a cikin gidan gwamnatin jihar Kano.

Onu, wanda ke cikin mashiryan gudun famfalaki na cibiyoyin yaki da rashawa na kasa a Abuja, ya ce wannan matakin da Ganduje ya dauka na bayyana hanya tagari da ya kama don toshe rashawa a jihar.

"Muna farin ciki da kokarin Gwamna Ganduje na yaki da rashawa kaca-kaca a jihad Kano. Ba a baki kadai ba, ya kirkiri ofisoshin yaki da rashawa a duk kananan hukumomin jihar. Wannan na nuna cewa, jihar Kano za ta zama shugaba a yaki da rashawa," in ji Onu.

DUBA WANNAN: Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi (Hotuna)

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasir Yusuf Gawuna ne ya karba lambar yabon a madadin gwamnan. Ya ce, gwamnatin jihar Kano karkashin Ganduje ta hada kai ne da Shugaban kasa Muhammadu Buhari don fatattakar rashawa.

Ya jinjinawa Onu da kungiyarsa ta yadda suka yi imani da gwamnatin Shugaba Buhari da duk matsayoyinta.

Gawuna ya kara da jinjinawa Onu da kungiyarsa a kan karramawa tare da gane cewa Gwamna Ganduje na yaki da rashawa.

Ya tabbatar wa da jama'ar Kano cewa, gwamnatin Ganduje zata cigaba da mayar da Kano jiha mai cike da 'yan kasa masu bin doka. Ya jaddada cewa, masu karya doka su sauya salo don kuwa jihar Kano bata da ma'adanar masu laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel