Yadda matar aure ta daba wa mijinta wuka a kahon zuciya don ya hana ta yin yaji

Yadda matar aure ta daba wa mijinta wuka a kahon zuciya don ya hana ta yin yaji

Jami'an hukumar 'yan sandan kasar Kenya ta cafke wata mata mai suna Mercy Wanjiru wacce ake zargi da soka wa mijinta mai suna Kevin Kuria wuka a kirji saboda ya hana ta barin gidansu na aure da sunan yaji.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba, a yankin Nakuru dake kasar Kenya yayin da Mercy ta kwashe kayanta domin barin gidan mijinta bayan fada-fadacen da suka saba yi sun ki ci sun ki cinye wa.

Ganau ba jiyau ba sunce Mercy wacce ta soki mijinta a kirji ta ce ta yi hakan ne domin kokarin kare kanta bayan da mijinta, Kelvin, ya nemi sukarta da wuka.

Daniel Thiongo ya ce: "An ga akwatinta dankam da kaya amma mijinta ya hana ta tafiya, a lokacin da aka kirani don insa baki domin sulhunta su. Amma da na isa gidan sai naga Kelvin a kwance a kasa, jini yana zuba daga kirjinsa."

DUBA WANNAN: Kotu ta bada umurnin ajiye jigo a APC a gidan yari kan yi wa gwamnan PDP kazafi

An kara gano cewa, wacce ake zargi da kisan kan ta dinga kiran makwabta da abokai don neman taimakon a kaishi asibiti.

An mika gawar mamacin zuwa asibitin Nakuru don adana ta, yayin da ita kuma Mercy aka garkame ta a ofishin 'yan sanda.

Kwamandan ofishin 'yan sandan Nakuru, Stephen Matu ya ce: "A halin yanzu, ana cigaba da bincike kuma za a mika wacce ake zargi gaban kuliya a ranar Juma'a domin ta fuskanci tuhume - tumen da ake yi mata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel