Me yayi zafi? Amarya ta fada rijiya ana gobe bikinta a jihar Kano

Me yayi zafi? Amarya ta fada rijiya ana gobe bikinta a jihar Kano

- Wata matashiyar budurwa mai shekaru 16 ta afka rijiya ana gobe ranar daurin aurenta

- Fadima amarya ta fada rijiya ne a yayin da suka je gidan mawankiya don wankan aurenta

- Angon marigayiya Fadima bai iya magana ba saboda halin alhini da yake ciki

Wata matashiyar budurwa mai shekaru 16 ta afka rijiya ana gobe ranar daurin aurenta. Lamarin ya faru ne a garin Gajaja na karamar hukumar Dambatta da ke jihar Kano a arewacin Najeriya.

Fadima amarya ta fada rijiya ne a yayin da suka je gidan mawankiya don wankan aurenta. An gano cewa, ta fada rijiyar ne a rashin sani.

Kanin marigayiyar amaryar ya bayyanawa BBC cewa, a yau Alhamis ne aka shirya daura mata aure da angonta amma sai kaddara ta ratsa.

DUBA WANNAN: Albishir: Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta janye yajin aikin da ta fara

“Auren soyayya ne, ita tana so, shima yana so. Yanzu haka da ake magana, ‘yan biki ne dankam a wurin zaman makoki,” cewar Alhaji Abubakar.

Ya kara da cewa, a halin yanzu suna kokarin shawo kan Hajiya Lami, wadda ita ce mawankiyar amaryar kuma kanwa ga mahaifiyar amaryar. A halin yanzu ko abinci ta kasa ci.

BBC ta samu jin ta bakin Hajiya Lami, inda ta ce tsautsayi ne ya faru wanda kuma baya wuce ranarsa.

Kanin angon mai suna Labaran, ya ce iyayen amaryar mazauna garin Babura ne na jihar Jigawa, kuma Fadima ta je garin Dambatta ne a shirye-shiryen bikin nata.

Angon marigayiya Fadima bai iya magana ba, saboda halin alhini da tsananin damuwa da yake ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel