Kano: Magidanci ya zubawa danshi shinkafar bera ya mutu, saboda ya haifeshi ba ta hanyar aure ba

Kano: Magidanci ya zubawa danshi shinkafar bera ya mutu, saboda ya haifeshi ba ta hanyar aure ba

- Jami'an 'yan sandan jihar Kano sun kama wani magidanci da ya kashe danshi

- Mutumin an kama shi ya zuba wa dan nashi mai shekaru uku shinkafar bera

- Da aka tambayeshi dalilin yin haka sai yace yayi hakan ne saboda ba ta hanyar aure ya samu yaron ba

Jami'an hukumar 'yansan jihar Kano sun samu nasarar kama wani mutumi magidanci, inda suke tuhumar sa da kashe dansa na cikinsa mai kimanin shekaru uku.

Mutumin da aka bayyana sunanshi da Musbahu, wanda yake zaune a unguwar mahaukaci dake karamar hukumar Gaya cikin jihar Kano, ya sanyawa dan nasa shinkafar bera a cikin abinci, inda yaron na ci yace ga garinku nan.

A hirar da mutumin yayi da wakilin freedom rediyo dake Kano, magidancin ya bayyana cewa yayi wannan aika-aika ne saboda dan nashin ba ta hanyar aure ya same shi ba, sannan kuma babu wata wacce za ta rike masa yaron, wannan dalilin ne yasa ya sanya masa guba a cikin abinci ya ci ya mutu.

KU KARANTA: Wa'iyazubillah: An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan yaje an sauya masa kama irin ta Annabi

Sai dai kuma magidancin ya nemi ayi masa sassauci akan laifin da ya aikata.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ta jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa da sun kammala binciken su akan wannan magidanci za su mika shi gaban kuliya domin ya fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.

Wannan dai ba shine karo na farko da irin haka take faruwa a Najeriya ba, sau da dama an sha kama uba ya kashe danshi ko kuma da ya kashe mahaifinshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel