Majalisar sarakuna: Ganduje ya bada umarnin gyaran gidan shettima

Majalisar sarakuna: Ganduje ya bada umarnin gyaran gidan shettima

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ba kwamishinan aiyuka da habaka ababen more rayuwa, Injiniya Mu’azu Magaji, umarnin gyaran ofishin majalisar sarakuna, Gidan Shettima, wanda yake a farfajiyar fadar Sarkin Kano.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, yin hakan na daga cikin shirye-shiryen kafa majalisar sarakunan a jihar Kano.

A wata takarda da babban sakataren yada labarai na Gwamna ya fitar a ranar Alhamis, Abba Anwar ya bayyana cewa, wannan umarnin alamu ne dake nuna cewa, rantsar da sarakunan za a yi shi nan ba da dadewa ba.

Takardar ta ce, Gwamna ya ba kwamishinan umarnin tabbatar da anyi gyaran a gaggauce. Tuni dai aka duba Gidan Shettima din don gano yanayin gyaran da za a yi.

“Ba gyara kadai ba, inason ganin aiki mai inganci. Saboda jihar Kano ta cancanci hadaddiyar majalisar sarakuna,” ya kara da cewa.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano zata yi doakar hana aurar da 'yammata kafin su kammala sakandire

Idan zamu tuna, gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani a kan hukuncin wucin gadi da wata babbar kotun jihar ta yanke a kan dokar kafa majalisar sarakunan jihar.

A wani jawabi mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labaran jihar, Malam Muhammad Garba, gwamnatin Kano ta ce hukuncin kotun bai shafi sabbin masarautun jihar da aka kirkira ba.

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa wata babbar kotun jihar Kano a karkashin Jastis Tijjani Bdamosi ta yanke hukuncin dakatar da gwamna Ganduje daga kafa majalisar sarakuna da kuma nada mambobin tare da tsayar da ranar 17 ga watan Disamba domin cigaba da sauraron karar.

A jawabin da gwamnatin ta fitar ranar Laraba, kwamishinan ya zargi makiya sabbin masarautun da aka kafa da sauya ma'anar hukuncin tare da bayyana cewa zasu sha kunya a karshe, bayan kotu ta yanke hukunci na karshe a kan batun.

Jawabin ya kara da cewa babu shakka bangaren gwamnati ne zai yi nasara a karshe saboda an bi doka wajen kirkirar sabbin dokokin masarautu a jihar Kano.

Kwamishinan ya bukaci jama'ar jihar Kano da su zauna lafiya tare da cigaba da yin biyayya ga doka a yayin da kotu ta zartar da hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel