Gwamnatin Jigawa za ta kashe naira miliyan 60 wajen gina dakunan ‘ba haya’

Gwamnatin Jigawa za ta kashe naira miliyan 60 wajen gina dakunan ‘ba haya’

Gwamnatin jahar Jigawa a karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Abubakar Badaru ta amince da kashe naira miliyan 60 wajen gina da kunan wanka da ba-haya a wasu kananan hukumomin jahar guda uku, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan ruwa na jahar Jigawa, Ibrahim Hannun-Giwa ne ya bayyana a ranar Laraba, 11 ga watan Disamba a garin Hadejia yayin ziyarar daya kai ma Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar-Maje.

KU KARANTA: Jiragen yakin Najeriya sun yi ma yan Boko Haram luguden wuta, sun konasu kurmus

Kwamishina Hannun-Giwa yace gwamnati za ta gina bandakunan ne a tashoshin motoci, kasuwanni, asibitoci, da sauraren amfanin jama’a a kananan hukumomin Auyo, Gagarawa da Kiyawa.

Kwamishinan ya kara da cewa manufar samar da wadannan dakunan ba haya shi ne domin kawo karshen yin ba haya a bainar jama’a da ake yawan yi a wadannan kananan hukumomi guda uku.

Wakilin kwamishinan a yayin wannan ziyarar, kuma babban sakatare a ma’aikatar, Nasiru Mahmud, ya yi kira ga mai martaba Sarkin Hadejia da ya gargadi jama’asa daga yin ba haya a bainar jama’a, tare da nuna musu hadduran dake tattare da haka, da suka hada da wanzan da cututtuka a tsakanin al’umma.

A nasa jawabin, Sarkin Hadejia, ta bakin wakilinsa, Galadiman Hadejia, Alhaji Usman Abdulazeez, ya tabbatar ma kwamishinan cewa masarautar Hadejia a shirye take ta bayar da gudunmuwa da goyon baya ga kawo karshen yin ba haya a bainar jama’a a jahar gabaki daya.

Sa’annan ya yi alkawarin sanar da sauran hakiman masarautar da dakatai domin su dabbaka wannan umarni. Daga karshe shugaban karamar hukumar Auyo, Uma Musa-Kalgwai yay aba ma kokarin gwamnatin na kawo karshen ba haya a bainar jama’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel