Cike da alfahari: Hotunan Buhari da Hanan bayan ta kammala digiri da sakamako mafi daraja
Hanan Buhari, 'yar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wallafa hotunanta tare da shugaban kasar. A cikin kwanakin nan ne Hanan ta kammala digirinta daga jami'ar Ravensbourne da ke Landan a fannin daukar hoto. Ta kammala digirin ne da sakamako mai daraja ta farko, wanda turawa ke kira da 'first class'.
Ta wallafa hotunanta tare da mahaifinta shugaban kasa Muhammadu Buhari. Mahaifin na kallon 'yar tashi ne cike da alfahari.
Legit.ng ta ruwaito yadda uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta wallafa kyawawan hotunanta tare da Hanan Buhari a yayin murnar kammala digirinta na farko daga wata jami’a a UK. Rahoto ya nuna cewa, Hanan ta kammala ne da digiri mai daraja ta farko.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Kotu ta yanke wa matar da ta kashe kishiyarta da 'ya'yan ta 7 hukuncin kisa
A wallafar da tayi a shafinta, uwargidan shugaban kasar ta bayyana yadda ‘yan uwa da abokan arziki suka taya su murnar wannan nasarar. An yi bikin yaye ta ne a makarantar a yau Talata 3 ga watan Disamba.

Asali: Facebook
Mahaifiyar cike da murna tare da tunkahon wannan nasarar, ta mika godiyarta ga jama’ar jihar Kebbi da suka hada da gwamnan jihar tare da uwargidansa a kan rawar da suka taka wajen aikin karshen da Hanan ta yi jami’ar.
Daga hotunan, Zahra Buhari da maigidanta duk sun hallara a wajen taron. An hango ‘yan uwa da abokan arziki duk a hotunan. Wacce ta kammala digirin, ta bayyana rike da shaidar kammala digirin a hannunta.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng