Yan Boko Haram sun kashe wani babban kwamandan Sojin Najeriya a filin daga

Yan Boko Haram sun kashe wani babban kwamandan Sojin Najeriya a filin daga

Wani babban kwamandan yaki na rundunar Sojan kasa ta Najeriya ya gamu da ajalinsa yayin da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka dasa wani bom a kusa da motarsa wanda ya tashi da shi, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a garin Marten a jahar Borno kamar yadda wasu majiyoyi na karkashin kasa daga rundunar Sojan suka tabbatar, inda suka ce jami’in Sojan shi ne kwamandan bataliya ta 153 dake Marte.

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma yan Boko Haram rakiyar Kura, sun ceto mata da kananan yara

Majiyoyin sun kara da cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, 7 ga watan Disamba yayin da kwamandan yake jagorantar Sojojinsa zuwa aikin sintiri, a daidai wannan lokaci ne bom din ya tashi da motar kwamandan.

Wasu majiyoyi na daban sun tabbatar da mutuwar kwamandan, amma sun ce babu tabbacin ko shi kadai ne ya mutu, ko kuma akwai wasu Sojoji na daban basu mutu ba, sai dai majiyarmu ta ki bayyana sunan mamacin sakamakon babu tabbacin ko iyalansa suna da masaniya ko kuwa a’a.

A wani labarin kuma, akalla dan Boko Haram daya ne ya gamu da ajalinsa a sakamakon wata arangama da aka yi tsakanin dakarun rundunar Sojin Najeriya tare da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a jahar Borno.

Jami’in kula da watsa labaru na Operation Lafiya Dole, Kanal Aminu Iliyasu ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba inda yace an yi dauki ba dadin ne a kauyen Malam Fatori cikin karamar hukumar Abadam na jahar Borno.

Kanal Aminu yace dakarun runduna Soja ta 68/94 ne suka kaddamar da samame a mafakar yan ta’addan Boko Haram dake kauyen, wanda hakan yasa bayan sun sha wuta yan ta’addan suka ranta ana kare, amma Sojoji basu kyalesu, sai da suka musu rakiyar Kura.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel