Yadda wani mutum ya mayar da kansa 'kujera' don matarsa mai juna biyu ta zauna a kansa

Yadda wani mutum ya mayar da kansa 'kujera' don matarsa mai juna biyu ta zauna a kansa

- Wani miji ya mayar da kanshi kujerar gajiyayyar matarsa mai juna biyu

- Matar mai tsohon ciki ta gaji ne da tsayuwa yayin jira layi ya zo kanta na ganin likita

- Jami'an ‘yan sandan kasar China ne suka yada bidiyon matar da mijinta

Wani bidiyon mutumin da ya zama kujera ga matarshi mai tsohon ciki ya taba zukatan mutane da dama. Matar ta dare bayan mijin ne tamkar kujera a lokacin da ta gaji da tsayuwa wajen jiran ganin likita

Bidiyon ya yawaita ne a yanar gizo bayan da ‘yan sandan kasar China suka fitar dashi. Bidiyon ya nuna wata mata mai tsohon ciki ne a gajiye kuma ta kasa tsayuwa saboda yadda kafafunta suka kumbura. Tana kan layin ganin likita ne a asibiti.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sanatoci da ministoci da kotu ta ce su dawo da fanshon da suka karba a matsayin tsaffin gwamnoni

Matar mai juna biyun bata samu wanda ya sauka daga kujerarsa ya bata don tausayawa halin da take ciki ba. A maimakon haka, tuni mijinta ya durkushe ta kuma haye bayansa. Ta zauna ne tare da rike wani karfe don ta ji dadin zaman nata.

Mijin bai tsaya a nan ba, masoyin mijin nata ya mika mata gorar ruwa don tabbatar da cewa bai bar matarsa cikin kishi ba a yayin jiran likitan.

Jami’an ‘yan sandan yankin Heilongjiang dake arewa maso gabas din kasar China ne suka wallafa a shafinsu. A kasan hoton, sun yi Alla-wadai da halin wadanda ke zaune a wajen kuma suka hana mai cikin matsuguni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel