Bidiyo: Saurayi na tsakar lalata da karuwa aljanunta suka tashi sai ya koma addu'a

Bidiyo: Saurayi na tsakar lalata da karuwa aljanunta suka tashi sai ya koma addu'a

- Kamar a wasan kwaikwayo abun ya faru a jihar Legas

- Wani matashi ya dauki karuwa mai jigida don kwanan gida, bayan komai ya kankama sai jigida ta tsinke

- A take dakin ya koma filin cire miyagun aljanu, don kuwa matashin ya tuna da Ubangiji

Abun ya koma kamar wasan kwaikwayon saboda yadda yanayin wajen ya sauya a take. An ajiye soyayyar jima'in an koma cire aljanu da addu'o'i tsakanin wata karuwa da kwastomanta.

Wannan sauyin yanayin ya auku ne a jihar Legas, lokacin da wani mutum ya dau karuwa mai jigida a kugu don kwanan gidan. A lokacin da suke gab da fara sha'ani, sun fara shafe-shafe da gabatarwa, sai jigidar ta tsinke daga kugunta ta fadi kasa. A take ta fara hauka inda ta koma wani abu daban.

Matashin ya yi zaton hakan na daga cikin dabarunta na kwanciya da namiji, amma sai ta fara bayyana hauka kiri-kiri. A take mutumin ya tuna Ubangiji sannan ya fara janyo ayoyi daga littafi mai tsarki don fitar da shaidanun da ke kan karuwar.

KU KARANTA: Babu dan kudun da zai zama shugaban kasa a 2023 ba tare da Buhari ya taimaka masa ba - Rochas Okorocha

Daga karuwar har matashin duk suna tsirara ne, kuma sun mayar da dakin filin waraka. Ya kara da gayyato abokinshi don addu'ar cire miyagun shaidanun da ke kan karuwar.

An cigaba da addu'ar har zuwa lokacin da karuwar ta fara fallasa kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel