Jerin sunayen sanatoci da ministoci da kotu ta ce su dawo da fanshon da suka karba a matsayin tsaffin gwamnoni

Jerin sunayen sanatoci da ministoci da kotu ta ce su dawo da fanshon da suka karba a matsayin tsaffin gwamnoni

Najeriya na fuskantar matsalar kudin shiga, wannan dalilin ne yasa gwamnatin tarayya ke jaddada bukatar biyan haraji.

Baya ga Karin kudin haraji da gwamnatin tayi daga kasha 5 zuwa 7.5, gwamnatin ta kirkiro da saka haraji a kan tura kudi ko fitarwa a bankuna, ta fara maganar dawo da toliget a manyan titunan tarayyar.

Gwamnatocin jihohi sune wadanda matsalar rashin kudin shiga ya fi damu. Jihohi kalilan ne suke iya dogaro da abinda gwamnatin tarayya ke basu a wata, kamar yadda rahoton wata kungiya mai kula da kasafin kudin gwamnatocin jihohi ta nuna.

A shekarar 2016, abin ya kai inda ya kai. Hakan ne yasa gwamnatin tarayya ta ba gwamnatocin jihohi dan wani hasafi don samun biyan bashin albashi da ma’aikata ke binsu.

A cikin wannan tsananin ne aka samu wasu ‘yan siyasa da suka bayyana son kansu kiri-kiri. Wannan son kai kuwa ya biyo bayan wasu dokokine da zasu iya kawo girgiza a tattalin arzikin kasar sannan su azurta ‘yan siyasar.

‘Yan siyasar da abun ya shafa sun hada da tsoffin gwamnoni, ministoci da sanatoci. Wasu daga cikinsu sun bar wani mukamin siyasa inda suka koma wani. A takaice dai suna kan kujerar gwamnatin. Amma sai suke komawa suna karbar kudin fansho na kujerar gwamnatin da suka karba. Suna kuma kara hadawa da kudin albashinsu na kujerar da suke kai.

A don haka ne babbar kotun tarayya da ke zama a Legas ta nukaci wadannan ‘yan siyasar da su hanzarta dawo da kudin fanshon da syka karba yayin da ssuke kan kujerar siyasa.

Ga jerin sunayensu:

1. Bukola Saraki (tsohon gwamnan Kwara, tsohon sanata)

2. Godswill Akpabio (tsohon gwamnan Akwa Ibom, tsohon sanata, a yanzu minista)

3. Rabiu Kwankwaso (tsohon gwamna, tsohon minista, stohon sanata)

4. Theodore Orji (tsohon gwamna, a yanzu sanata)

5. Abdullahi Adamu (tsohon gwamnan Nasarawa, a yanzu sanata)

6. Sam Egwu (tsohon gwamnan Ebonyi, a yanzu sanata)

7. Shaaba Lafiagi (tsohon gwaman Kwara, tsohon sanata)

DUBA WANNAN: Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

8. Joshua Dariye (tsohon gwamnan Filato, tsohon sanata, amma yanzu yana gidan gyaran hali saboda almundahanar kudade)

9. Jonah Jang (tsohon gwamnan Filato, tsohon sanata)

10. Ahmed Sani Yarima (tsohon gwamnan Zamfara, tsohon sanata)

11. Danjuma Goje (Tsohon gwamnan Gombe, tsohon minista, sanata a yanzu)

12. Bukar Abba Ibrahim (tsohon gwamnan Yobe, tsohon sanata)

13. Adamu Aliero (tsohon gwamnan Kebbi, tsohon minista, a yanzu sanata)

14. George Akume (Tsohon gwamna Benuwe, tsohon sanata, a yanzu minista)

15. Biodun Olujimi (Tsohon mataimakin gwamnan Ekiti, sanata a yanzu)

16. Enyinaya Harcourt Abaribe (tsohon mataimakin gwamnan Abia, sanata a yanzu)

17. Rotimi Amaechi (Tsohon gwamnan Ribas, minista a yanzu)

18. Kayode Fayemi (Tsohon gwamna, tsohon minista, gwamna a yanzu)

19. Chris Ngige (Tsohon gwamnan Anambra, tsohon sanata, minista a yanzu)

20. Babatunde Fashola (Tsohon gwamna Legas, minista a yanzu)

A halin yanzu, kotun ta umarci Abubakar Malami, da ya fitar da hanyoyin da shari’a ta tanadar don kalubalantar wadannan dokokin da suka ba ‘yan siyasar damar karbar albashi tare da kudin fansho a laokaci daya.

Tuni dai gwaman jihar Zamfara ya kankare wannan dokar ta biyan alawus da fansho ga tsoffin ‘yan siyasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel