Gwamna Badaru zai fara biyan ma’aikatan jahar Jigawa karancin albashin N30,000

Gwamna Badaru zai fara biyan ma’aikatan jahar Jigawa karancin albashin N30,000

Gwamnatin jahar Jigawa ta bayyana cewa daga watan Disambar 2019 za ta fara biyan sabon karancin albashin N30,000 ga ma’aikatanta, inji rahoto kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan jahar, Muhammadu Badaru Abubakar ne ya bayyana haka a garin Dutse bayan ya rattafa hannu a kan dokar karancin albashin a ranar Laraba, 4 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Sule Lamido ya bayyana gaskiyar abin da ake biyansa a matsayin fansho

An cimma yarjejeniyar biyan kudin tare da tsare tsaren matakan karin albashin ne a tsakanin shuwagabannin kungiyar kwadago na jahar Jigawa da hadakar jami’an hukumomin gwamnati.

Mataimakin gwamnan jahar Jigawa, Umar Namadi ne ya rattafa hannu a kan dokar a madadin Gwamna Badaru, yayin da Sanusi Alhassan da Hassan Auwalu, shuwagabannin bangarorin da suka shirya yarjejeniyar suka rattafa hannu a madadin bangarorinsu.

“Mun cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa a tsakanin masu ruwa da tsaki, don haka na yaba da kokarin da suka nuna wajen tabbatar da wannan lamari, kuma ina tabbatar muku zamu cigaba da biyan albashi a ranar 25 na kowanne wata kamar yadda muke yi tun shekaru 4 da suka gabata.

“Don haka daga yau na baiwa sakataren gwamnati da shugaban ma’aikatan jahar Jigawa su fara shirin ganin an biya sabon karancin albashin a watan Disamba.” Inji shi.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar kwadago na jahar, ya jinjina ma gwamnan bisa cika alkawarin daya dauka na dabbaka sabon karancin albashin N30,000. Sa’annan ya kara da cewa ma’aikata daga mataki na 01-06 zasu samu N30,000, yayin da yan mataki na 07 zuwa sama zasu samu karin kashi 23 zuwa 12.

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya cewa a matsayinsa na tsohon gwamnan jahar Jigawa, N667,000 kacal ake biyansa a matsayin kudin fansho a duk wata, amma duk da karancin kudin, tsawon shekara daya kenan ko sisi bai gani ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel