Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

Wata mata mai bukatar saki mai suna Blessing Abu, ta zargi mijinta mai suna Benjamin da laifin cin amanarta. Benjamin ya roki kotun da kada ta kashe aurensu.

A ranar Laraba ne Blessing ta bayyana da kokenta a gaban kotun da bukatar janye kararta.

Ta roki kotun da kada ta cigaba da sauraron karar kuma zasu sasanta da mijinta.

Shugaban kotun, Adeniyi Koledoye, yayin soke karar, ya yi kira ga ma'auratan da su zauna lafiya tare da rayuwa cike da soyayya da kaunar juna.

"Kotun ta samu wasikar mai bukatar janye karar wacce mai koken ta kawo. A don haka ne kotun ta soke karar,"

"Na yi kira gareku da ku koma gida kuma ku rayu cikin lumana da soyayya," in ji shi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Blessing Abu ta tunkari kotun ne don warware aurensu mai shekaru 12 saboda cin amanarta da mijinta ke yi.

"Mijina na cin amanata, ya durawa wata yarinya ciki har sau biyu. Na je gidajen magani da asibitoci kala-kala don samun haihuwa. Amma mijina yana can yana dirkawa 'yan mata ciki,' ta jajanta.

Telar mai shekaru 36 ta zargi mijinta da hanata hakkinta na aure.

DUBA WANNAN: Dalla-dalla: Ɗan majalisar APC ya bayyana kudaden da ya ke karba duk wata

"Mijina baga bani hakkina, duk da ina bukatar haihuwa. Daga bisani ya umarceni da in nemi wani namijin ya kwanta dani, amma shi ba zai sake kwanciya dani ba," ta zarga.

Blessing fa zargi mijinta da yin barazana kala-kala ga rayuwarta.

"Benjamin ya ce in bar gidanshi ko ya zuba min guba a abinci. Zai kasheni ko kuma zan haukace," ta sanar da kotun.

Mai karar ta roki kotun da ta tsinke igiyar aurensu don ta dena son mijin.

A yayin mayar da martani a kan zarginsa da ake, Benjamin mai shekaru 42 ya zargi matarsa ta turashi zuwa neman mata.

"Mata ta sanar dani cewa ban isa inyi wa wata ciki ba. Idan na yi kokarin kwanciya da wata mace, mazakuta ta zata makale a jikinta. Ta ce min ta asirceni a kan hakan. Da farko naji tsoro, amma daga baya na gwada don tabbatar da zancenta."

"Sa'ar da nayi kuwa, har ciki nayi wa wata kuma ta haihu. Lokacin da matata ta sani, sai tace min abinda muka haifa ba nawa bane. Bayan watanni na kara gwadawa kuma yarinyar ta samu ciki," in ji shi.

Ya cigaba da cewa, "tun daga nan Blessing ta hanamu zaman lafiya. Ta kira 'yan sands aka kamanjn, da naga ba zan iya ba sai na kwashe kayana na bar gidan," in ji shi.

Wanda ake karar ya ce matarshi ta hanashi kwanciya da ita saboda tace tana ciwon ka idan haka ta faru. Ya roki kotun a kan kada ta kashe auren, don yana kaunarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel