An ci tarar matashi shanu 3 bayan samunsa da laifin lalata da kishiyar mahaifiyarsa

An ci tarar matashi shanu 3 bayan samunsa da laifin lalata da kishiyar mahaifiyarsa

An ci tarar wani matashi shanu guda uku bayan ya amsa laifin cewa ya yi lalata da kishiyar mahaifiyarsa da kuma wasu matan aure masu yawa.

An samu matashin, Albert Musokeri, mai shekaru 25, da laifin lalata da kishiyar mahaifiyarsa, Ketina Musokeri, mai shekaru, 35 a garin Gokwe da ke kasar Zimbabwe.

Wata majiya mai kusanci da gidan da abun ya faru ta ce Albert da Ketina sun shafe fiye da shekaru biyu suna kwanciya tare ba tare da sanin mahaifinsa ba.

"Albert da kishiyar mahaifiyarsa sun shafe kusan shekaru biyu suna soyayya ba tare da mahaifinsa, Joshua Musokeri, ya sani ba, sai yanzu da asiri ya tonu.

"Akwai lokacin da yake zargin cewa matarsa na cin amanarsa amma bai yi tunanin cewa tana aikata hakan da dan cikinsa bane.

"Musokeri ne da kansa ya kama matarsa da dansa suna lalata. Watarana ne Musokeri ya bi bayan Ketina yayin da ta tafi debo ruwa a bayan gari. Yana biye da ita ne sai ya ga ta ratse zuwa cikin wata duhuwa a cikin jeji, kuma da ya lallaba don ganin me take yi a wurin, sai ya same ta turmi da tabarya da dansa suna lalata.

" Musokeri ne ya sanar da maigari abinda ya faru, shi kuma ya mika maganar ga jami'in hukuma, Cif Chireya," a cewar majiyar.

Chief Chinyere ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

"Ina mai tabbatar muku da cewa nine na tuhumi wani laifi mai ban mamaki inda aka samu wani ya shigar da korafi bayan ya kama matarsa da dan cikinsa suna lalata a jeji.

"Shi da kansa dan mutumin ya amsa lafinsa, ya fada da bakinsa cewa ya kwanta da kusan rabin matan aure da ke kauyensu," a cewar Cif Chireya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel