Gwamnan Zamfara ya roki Allah Ya saukar da masifa a kan masu keta alfarmar Al-Qur’ani

Gwamnan Zamfara ya roki Allah Ya saukar da masifa a kan masu keta alfarmar Al-Qur’ani

Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara ya yi addu’ar Allah Ya saukar da fushinsa a kan duk masu cin mutuncin Al-Qur’ani a jahar Zamfara, sa’annan ya yi kira ga al’ummar jahar Zamfara dasu cigaba da rokon Allah a kan wannan matsala.

Matawalle ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 2 ga watan Disamba yayin bude taron gasar Al-Qur’ani mai girma na shekarar 2019 daya gudana a garin Gusau inda yace:

“Wannan addu’an ya zama wajibi saboda masu aikata laifin nan sun tafka mummunan badala wand aka iya janyo mana masifa, don haka haka muyi addu’a kada fushin Allah Ya shafemu.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta dauki nauyin biyan kudin WAEC da NECO ga dalibai 5000 a Adamawa

“A matsayina na gwamna, na kafa kwamitin bincike, kuma duk wanda muka kama da laifi sai ya fuskanci hukunci kamar yadda dokokin shari’ar musulunci suka tanadar, duk girmansa kuwa.” Inji shi.

Matawalle ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci aikata badala ba, don haka ya umarci dukkanin hukumomin tsaro dake jahar dasu bude idanunsu, sa’annan su kama duk wanda ya karya doka domin ya fuskanci hukunci.

Sa’annan gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da kwamitin shirya gasar Al-Qur’anin, inda yace mutane ne masu ilimi da sanin ya kamata, kuma sun samu goyon bayansa yadda ya kamata, don haka ya yi kira ga yan kwamitin da su yi adalci wajen gudanar da aikinsu.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar, Alhaji Aminu Nahuche ya bayyana cewa zasu yi iya bakin kokarinsu don ganin sun zabo gogaggun mahaddata wadanda zasu iya wakiltar Najeriya a gasar duniya gaba daya.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito an fara gasar ne a watan Oktoba a kananan hukumomin jahar 14, daga nan aka zabo zakarun da zasu fafata a matakin jaha, daga cikinsu kuma za’a ware zakaran da zai wakilci jahar a matakin kasa a shekarar 2020.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel