Shikenan: Mutumin da ya shafe shekaru 12 a gidan yari akan laifin da bai aikata ba yanzu ya zama lauya

Shikenan: Mutumin da ya shafe shekaru 12 a gidan yari akan laifin da bai aikata ba yanzu ya zama lauya

- Wani kalubalen a rayuwa, alamar nasara ce da ke tunkaro dan Adam. Nasara kuwa bata zuwa sai da hakuri mai yawa

- Wani mutum mai suna Akpoghene Edeno ya amsa kiran zama lauyan Najeriya bayan shekaru 12 da yayi a gidan yari

- An zargi mutumin ne da kisan kai da bashi ya aikata ba. Bayan fitowarshi daga gidan yarin ne ya samu gurbin karatu a jami’a

Allah mai iko da buwaya. Wani dan Najeriya da ya yi shekaru 12 a gidan gyaran hali a kan laifin da bai san hawa ba, bai san sauka ba ya zama lauya. Bawan Allah ya kammala karatunshi sannan ya amsa kira na zama lauya a Najeriya.

Charles Mallam-Obi wanda ya bayyana labarin abokinshi mai suna Akpoghene Edeno, ya ce an garkame shi ne gidan yari na shekaru 12 a kan kisan da ake zarginshi da shi.

Ya bayyana cewa, Edeno ya rubuta jarabawar kammala sakandirensa ne a lokacin da yake gidan gyaran hali. Ya kuma samu gurbin karatu a jami’ar jihar Benin don karantar fannin shari’a bayan da ya samu yancinshi a 2012.

KU KARANTA: San barka: Sarkin Kano Muhammadu Sanusi zai fitar da mahaddatan Al-Qur'ani karatu kasar waje

Ya rubuta “Akpoghene Edeno abokina ne na yarinta. Ya yi shekaru 12 a gidan maza saboda kisan da bashi ya aikata ba. Ya rubuta jarabawar WAEC a gidan yarin. Bayan fitowarshi a 2012 ne ya samu gurbin karatu a jami’ar Benin don karantar lauyanci. A yau ya amsa kiran zama cikakken lauyan Najeriya,”

“Labarinshi ya nuna yadda jajircewa da karfin hali na dan Adam yake da shi. Zai yuwu ranshi ya baci saboda irin rashin adalcin da aka yi mishi. Hakan zai iya sa mishi yankewar burikanshi. Amma kuma sai ya zabi fin karfin kalubalen rayuwa.”

Ina taya ka murna dan uwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel