Jami'an 'yan sanda sun kama maza 47 da ake zargi da luwadi

Jami'an 'yan sanda sun kama maza 47 da ake zargi da luwadi

'Yan sanda a jihar Legas sun gurfanar da maza 47 da ake tuhuma da laifuka masu alaka da luwadi. An gurfanar da su ne gaban babban kotun tarayya na jihar Legas kan zargin aikata laifi guda daya na soyayya da jinsi daya.

'Yan sandan sun yi ikirarin cewa an kama wadanda akayi karar ne a wani otel da ke Egbeda a ranar 25 ga watan Augustan 2018 misalin karfe 2 na dare yayin da suke gudanar da wasu bukukuwan maraba da sabbin mambobi.

Sai dai dukkan wadanda aka yi karar sun musanta zargin da ake musu.

Bayan sun musanta aikata laifin, mai shigar da kara, Mista J.I. Ebhoremen ya nemi kotun ta bayar da umurnin cigaba da tsare su a hannun hukuma.

Sai dai lauyan da ke kare wadanda akayi karar ya nemi a bayar da belinsu kuma Mai shari'a Mohammed Aikawa ya ce duk da cewa zargin da ake musu ba karami bane, hakan ba zai hana a bayar da belinsu ba.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

Hakan yasa ya bayar da belin kowanne dayansu kan kudi N500,000 da mutane biyu da za su tsaya wa kowannensu.

Alkalin ya ce dole duk wanda zai tsaya musu ya kasance ma'aikacin gwamnati da ya kai matsayi na 10 zuwa sama yayin da dayan kuma ya zama mai sana'a ta gari da albashi da kotun za ta iya tabbatarwa.

Ya kuma bukaci dukkan wadanda aka yi karar su saka hannu kan yarjejeniyar cewa ba za su aikata wani abu da zai kawo cikas ga shari'ar ba.

Aikawa ya kuma ce a bawa wadanda aka yi karar masauki a caji ofis din 'yan sanda na tsawon awanni 48 kafin a cika ka'idojin belinsu kuma a mika su zuwa gidan gyaran hali idan sun gaza cika ka'idojin belin da kotu ta gindaya musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel