'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

Tun da Najeriya ta dawo tafarkin mulkin demokradiyya na jahuriyya ta 3 a shekarar 1999 dai jam'iyyar Peoples Democratic Party ce ke mulkin kasar inda Shugaban Olusegun Obasanjo ya yi shekaru 8, sannan ya mika wa marigayi Shugaba Musa Yar'adua sannan sai Shugaba Goodluck Jonathan.

A shekarar 2015 ne jam'iyyar hamayya ta APC ta yi nasarar hambarar da gwamnatin PDP inda shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan kujerar shugabancin kasa kuma ya sake cin zabe a 2019 ya zarce karo na biyu inda ya kayar da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Sai dai masu nazarin siyasa a Najeriya suna ganin akwai yiwuwar jam'iyyar ta PDP tana da damar kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 duba da cewa wa'adin mulkin Shugaba Buhari za ta zo karshe kuma samun shugaba irin mai kwarjini da farin jininsa ba abu ne mai sauki ba.

A wannan rubutun, za muyi nazarin wasu 'yan siyasar ake ganin idan har jam'iyyar ta PDP za ta tsayar da su takara akwai yiwuwar su iye karbe mulki daga jam'iyyar ta APC.

1. Atiku Abubakar/Peter Obi

Duk da cewa jam'iyyar ta PDP bata fito fili ta bayyana wadanda za ta tsayar domin takarar zaben na 2023, akwai yiwuwar maimaita 'yan takarar da ta gabatar a 2019 wato Atiku da Obi duba da cewa sun taka rawar gani a zaben amma ba su kai labari ba. Wani abu mai muhimmanci wurin tsayar da 'yan takara shine samun 'yan takarar da ke da arzikin da za su dauki nauyin kamfen, kwarewa a siyasa, farin jini da kuma karbuwa wurin al'umma.

Sai dai wani abu da ka iya kawo wa Atiku cikas shine batun shekarunsa duba da cewa a yanzu yana da shekaru 73 da haihuwa kuma a 2023 zai kasance yana da shekaru 77.

2. Aminu Tambuwal/Nyesome Wike

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto gogaggen dan siyasa ne kuma yana daya daga cikin wadanda suka fafata wurin neman tikitin takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar ta PDP a 2019. Tambuwal shine ya zo na biyu a zaben fidda gwani na PDP wadda hakan na nuna karbuwarsa a jam'iyyar da samun amincewar masu ruwa da tsaki a jam'iyyar.

Gwamna Tambuwal yana da alaka mai kyau tsakaninsa da Gwamna Nyesome Wike na jihar Rivers da shima jigo na a jam'iyyar duba da cewa ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin shugaban jam'iyyar na kasa Uche Secondus ya zama shugaban jam'iyyar. Hakan alama ce da ke nuna zai iya ruwa da tsaki wurin ganin sun samu tikitin takarar.

DUBA WANNAN: Bidiyon wani da ya fito da mazakutarsa ya yi barazanar yi wa ma'aikaciyar wutan lantarki fyade

3. Rabiu Musa Kwankwaso/Ben Ayade

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tabbas yana daga cikin 'yan siyasa masu farin jini a Najeriya musamman saboda irin tallafi da ya ke bawa matasa da jawo su a jiki a siyasarsa. Kwamkwaso yana daya daga cikin wadanda suka yi takarar neman tikitin shugaban kasa na PDP a 2019 amma bai kai labari ba.

Gwamnan jihar Cross Rivers, Farfesa Ben Ayade yana daya daga cikin gwamnonin johohin da ake yi wa kallon masu kwazo ne kuma wasu masu nazarin siyasa na ganin zai iya samar wa jam'iyyar kuri'un da ta ke bukata a kudancin Najeriya.

Saura da ke iya zama 'yan takarar jam'iyyar sun hada da Ibrahim Dankwambo da Ike Ekweremadu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel