Kishi: Yadda matar aure ta antayawa tsohuwar matar mijinta ruwan zafi a fuska

Kishi: Yadda matar aure ta antayawa tsohuwar matar mijinta ruwan zafi a fuska

An gurfanar da wata matar aure, Janet Ojukwu mai shekaru 41 a gaban kotu a Legas kan zargin ta da antayawa tsohuwar matar mijinra ruwan zafi a fuska.

Ana tuhumar Ojukwu mai zaune a Makoko a unguwar Yaba a Legas ta laifin yi wa wani a kotun Majistare da ke Yaba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai ta musanta aikata laifin da ke tuhumar ta da shi.

Mai gabatar da kara, Saja Godwin Oriabure ya shaidawa kotu cewa wanda ake karar ta aikata laifin ne misalin karfe 3 na yamma a ranar 3 ga watan Nuwamba a gida mai Lamba 7 Imamehin Street, Makoko, Yaba.

Oriabure ya ce wanda ta shigar da karar, Misis Grace Onuoha ta kai diyarta gidan tsohon mijinta ne domin ta karbo wasu tufafi yayin da wanda ake karar ta kai mata hari.

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda ake yi wa wata mata na zamani bilicin ya tayar da hankulan 'yan Najeriya

Ya ce Ojukwu ta zuba wa Onuoha ruwan zafi a fuskanta inda ta ke zargin cewa tana kokarin kwace mata miji.

Ya ce, "An garzaya da wanda ta yi karar zuwa asibiti inda aka bata gado."

Ya ce laifin ya sabawa sashi na 173 na dokar masu laifi na jihar Legas na 2015.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa sashi na 173 ya tanadar da hukuncin gidan yari na shekaru uku inda laifin yiwa wani rauni ya tabbata.

Shugaban kotun, Misis S.O. Obasa ta bayar da belin wanda aka yi karar kan kudi N20,000 tare da mutane biyu da za su tsaya mata.

Obasa ta ce wadanda za su tsaya mata su kasance masu sana'a kuma su nuna shaidan biyan haraji a jihar Legas na shekaru biyu.

Ta dage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 12 ga watan Disamban 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel