Rikicin duniya da mai rai ake yin ta: Miji ya zargi matarsa da kwanciya da maigidansu
Wani magidanci mai sana’ar tuka babbar mota, Azeez Hakeem ya shaida ma wata kotun gargajiya dake zamanta a garin Ibadan cewa matarsa Mufuli tana kwanciyar da mutumin dake mallakar gidan da suke zaman haya a cikinsa.
Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Hakeem ya shaida ma kotun haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba yayin da yake kare kansa daga zargin da matarsa ta yi masa na cin zarafinta.
KU KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta soke biyan tsofaffin gwamnoni miliyoyin kudaden fansho
A cewar Hakeem, a lokacin da matarsa ke dauke da cikin dansu na biyu, kwatsam sai maigidan nasu ya yi ikirarin cewa cikinsa ne, har ma ya yi rikici da shi wajen rada ma yaron suna, toh don haka idan ba rami mai ya kawo rami.
“Bayan haihuwar da nan a biyu, sai maigidan ya zo gidan iyayena yana ikirarin cewa dansa ne, kuma don haka shi ke da hakkin rada masa suna, da kyar aka warware wannan bahallatsa, amma duk da haka bata daina bin sa ba.
“Bata damu da ciyar da yaranta ba, bata dawowa gida sai tsakar dare, sai ta dinga fakewa da cewa tana zuwa sallah ne a masallaci, ko a lokacin da ta bar gidana, ni na kama mata haya domin ta dinga kulawa da yaranmu.” Inji shi.
Sai dai ita kuma Mufuli, ya shaida ma kotun cewa Hakeem ya mayar da ita tamkar jaka, abu kadan sai ya jibgeta, hatta a gaban yaransu, inda tace wannan shine dalilin barinta gidan mijin tun a shekarar 2016. Sai dai ta tabbatar ma kotun cewa bayan ta rabu dashi yi wani sabon saurayi.
Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkalin kotun, Cif Henry Agbaje ya bukaci ma’aurata su koma gida su warware matsalolinsu ko don albarkacin yaransu, sa’annan ya dage karar zuwa ranar 9 ga watan Disamba domin yanke hukunci idan sulhu bai yiwu ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng