Manyan 'yan majalisar PDP 3 da suka sha kaye a kotun daukaka kara

Manyan 'yan majalisar PDP 3 da suka sha kaye a kotun daukaka kara

Duk da cewa an kammala babban zaben 2019, har yanzu Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ba ta kammala aikinta ba.

Baya ga zaben gwamna da aka gudanar a jihohin Kogi da Bayelsa a ranar Asabar da ta gabata a ranar 16 ga watan Nuwamba, hukumar za ta gudanar da wasu zabukkan raba gardama na kujerun wasu 'yan majalisa.

Hakan ya faru ne sakamakon hukunce-hukuncen da kotunnan daukaka kara a sassa daban na kasar suka yanke na cewa INEC ta sake zabe a wasu wuraren bayan kwaje kujerun wasu 'yan majalisar.

Hukuncin na kotun ya shafi jam'iyyun APC da PDP baki daya. A wannan rubutun zai ni nazarin wasu manyan 'yan majalisar PDP ne da kotun daukaka kara ta soke zabensu.

1. Dino Melaye (Kogi West)

Kotun daukaka kara a Abuja ce ta soke zaben Sanata Dino Melaye mai wakilatan Kogi ta Yamma.

Kotun ta bayar da umurnin a sake yin zaben raba gardama a cikin kwanaki 90. Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ne ya kallubalanci nasarar Melaye a kotun. Duk da cewa an yi zaben raba gardama tare da zaben gwamnan jihar Kogi, ba a sanar da wanda ya lashe zaben ba domin INEC ta ce zaben bai kammalu ba wato 'Inconclusive'. INEC ta tsayar da ranar 30 ga watan Nuwamba don karasa zaben.

2. Lazarus Nweru Ogbee (Ikwo/Ezza South)

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Enugu a jihar Enugu ta kwace kujerar dan majalisa mai wakiltanIkwo/Ezza South a majalisar dokokin tarayya, Lazarus Nweru Ogbee.

Kafin a soke zabensa, Ogbee shine shugaban kwamitin yi wa gidajen gyaran hali garambawul.

Kotun ta jadada hukuncin da kotun zabe ta yanke a baya na cewa dan takarar jam'iyyar APC, kwamared Chinedu Ogah shine ya yi nasara a zaben.

Hakan yasa kotun ta umurci INEC ta bawa Chinedu Ogah na jam'iyyar APC takardan shaidan lashe zabe.

3. Sanata Christopher Ekpenyong (Ikot Ekpene)

Har ila yau kotun daukaka karar ta soke nasarar Sanata Christopher Ekpenyong mai wakiltan Ikot Ekpene na jihar Akwa Ibom a majalisar dokokin tarayya.

Kotun ta bayar da umurin sake yin zaben raba gardama a karamar hukumar Essien Udim na jihar cikin kwanaki 90.

Sanata Godswill Akpabio na jam'iyyar APC ne ya kallubalanci nasarar Ekpenyong a kotun daukaka karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel