Likita ya ceto ran dattijo a jirgin sama ta hanyar tsotse fitsari daga mararsa (Bidiyo)

Likita ya ceto ran dattijo a jirgin sama ta hanyar tsotse fitsari daga mararsa (Bidiyo)

- Wani likita mai kaifin tunani ya ceto ran wani dattijo yayin da suke tafiya a jirgin sama ta hanyar tsotse fitsarin da ke mararsa da bakinsa

- Likitan ya yi amfani da kayayyakin da ya samu a cikin jirgin saman ya cigaba da tsotse fitsarin dattijon na tsawon mintuna 37

- Dattijon ya kasance cikin ukuba domin ya kasa fitsari kuma kodarsa na dauke da fitsari kimanin 800ml

Matafiya sun shiga jirgin China Southern Airlines kamar yadda aka saba daga Guangzhou zuwa New York a kasar Amurka.

Sai dai a wannan ranar an samu afkuwar rashin lafiya na gaggawa yayin da wani dattijo ya tsinci kansa a cikin mawuyacin hali.

Dattijon ya kasa yin fitsari da kansa duk da cewa mafitsararsa ta cika da fitsari kimanin 800ml.

TimesLIVE ta ruwaito cewa daya daga cikin fasinjojin da ke jirgin mai zuna Zhang Hong, wadda likita ne mai tiyata ya yi jarumta ya kaiwa dattijon dauki.

Ya yi amfani da allurar sirinji, abin tsotso ababen sha wato 'straw' da kuma na'urar shakar iskar oxygen nan take ya fara zuko fitsari daga marar dattijon kuma ya cigaba da hakan har na tsawon mintuna 37.

DUBA WANNAN: Hotunan wasu takalman Buhari da ya dauki hankulan 'yan Najeriya a Twitter

Ga bidiyon likitan yayin da ya ke tsotso fitsari daga marar dattijon yana zubarwa cikin wani kwalba.

A cewar The South China Morning Post, akwai yiwuwar dattijon zai iya rasa ransa da Hong bai taimaka masa ba.

Legit.ng ta gano cewa likitan ya yi wannan aikin na gaggawa ne yayin da jirgin ke da ta tafiyar awanni shida a gabansa kafin su isa inda za su sauka.

Hong ya ce: "Da na lura cewa mutumin ba zai iya jure ciwon ba, abinda na ke tunani kawai shine yadda zan fitar da fitsarin da ke mararsa."

Source: Legit

Tags:
Online view pixel