Bidiyon yadda ake yi wa wata mata na zamani bilicin ya tayar da hankulan 'yan Najeriya

Bidiyon yadda ake yi wa wata mata na zamani bilicin ya tayar da hankulan 'yan Najeriya

Ma'abota amfani da shafin sada zumunta na Twitter sunyi mamaki tare da kaduwa bayan ganin wani faifan bidiyon yadda ake daye wa wata mace fata da sunnnan 'bilicin' wato kara hasken fata.

A cikin bidiyon da @BraQuaye_Gh ya wallafa a shafinsa na Twitter, an nuna wata mace tana kwance a bandaki a akwatin wanka cike da ruwa yayin da wata kuma ke daye fatan kafar ta.

A yayin da ta ke daye fatar, matan da ke aikin bilicin din tana tallatawa kanta har tana fadin adadin kudin da ta ke karba don yin wannan abinda ta kira 'wankin fata'.

Likitoci da sauran masu bincike sun sha gargadi kan shafa mayuka ko wasu ababe a fatan jiki da niyyar daye fata domin kara hasken fata da mafi yawanci bakaken mutane suka fi yin hakan.

DUBA WANNAN: Hotunan wasu takalman Buhari da ya dauki hankulan 'yan Najeriya a Twitter

Wadanda ke yin hakan suna aikatawa ne domin sha'awar fata mai haske sai dai masana sun ce hakan na karya garkuwar jiki tare da janyo afkuwar cututukan fata har ma da cutar kansa ta fata.

A wasu kasashen nahiyar Afirka ma an haramta sayar da duk wasu kayan shafe-shafe na yin bilicin.

@Cilla_ee, ta ce, "Menene aibin bakar fata? Ta yaya aka rude mu har muka fara tunanin cewa fatar da aka haife mu da ita ba ta da kyau. Kaico.

@EmaniMone, ta ce, "wannan kuwa ba zai yi zafi ba?

@Rama5825587 ya ce, "Wannan shine abu mafi mamaki da na taba gani

@louisadove, ta ce, "Haka ya ke, ni na kasa kallo har karshe ma.

@mslamz, ta ce, Allah ya taimake mu

@SoundsOfCartel, ya ce, ana daye mata fatar da ke mata garkuwa a jiki hakan zai saka cututuka su samu damar shiga jikinta. Duk saboda mene?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel