Wata sabuwa: Buhari ya juya ma ministan sharia baya a kan wata kwangila mai tsoka

Wata sabuwa: Buhari ya juya ma ministan sharia baya a kan wata kwangila mai tsoka

A wani mataki daya baiwa masu bibiyan siyasar Najeriya mamaki, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da wata kwangila da ministan sharia Abubakar Malami ya baiwa wata kamfani a kan aikin kwato kudaden Najeriya dake hannun kamfanonin dake hakar man fetir a Najeriya.

Jaridar The Cables ta ruwaito Buhari ya soke wannan gwaggwabar kwangila ne sakamakon rashin amincewa da makudan kudaden da gwamnati za ta biya kamfanin mai suna Trobell International Limited, kamar yadda ta yi yarjejeniya da minista Abubakar Malami.

KU KARANTA: Na himmatu wajen inganta rayuwar yan Najeriya – cewar shugaba Buhari

Malami ya baiwa kamfanin Trobell kwangilar amso dala biliyan 43 daga wajen kamfanonin dake hakar man fetir a cikin ruwan Najeriya, a madadin gwamnatin Najeriya, kamar yadda sabuwar dokar hakar man fetir a cikin ruwa ta tanada, kuma ya amince ya biyasu kashi 5 na kudin a matsayin kudin aikinsu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito idan aka lissafa kashi 5 na wannan kudi ya kai dala biliyan 2.15, wanda hakan ya yi daidai da zunzurutun kudi naira biliyan 774 a matsayin kudin da kamfanin Trobell za ta zaftara daga wadannan kudade da za ta amso ma Najeriya.

Sai dai cikin wata wasika da shugaban kasa ya aika ma minista Malami ta hannun shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Abba Kyari, ya umarce shi ya soke wannan kwangila daya baiwa kamfanin Trobell.

Majiyoyi daga Aso Rock Villa sun bayyana cewa shugaba Buhari ya yi mamakin wadannan makudan kudade da yace Trobell za ta kwasa daga aika ma kamfanonin wasikar cewa su biya gwamnatin Najeriya kudadenta kawai.

Haka zalika Buhari ya aika ma Malami tambayar cewa ta yaya suka cimma wannan kashi 5 da yake so a biya wannan kamfani, bayan tun farko gwamnati ma da kan ta za ta iya yin wannan aiki ba tare da daukan hayan wani kamfani ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel