Bayan ya gama wahalar budewa matarsa sabon shagon sayar da kaya, ranar da ya fara kawo mata ziyara ya tarar da ita da katon gardi suna lalata a ciki

Bayan ya gama wahalar budewa matarsa sabon shagon sayar da kaya, ranar da ya fara kawo mata ziyara ya tarar da ita da katon gardi suna lalata a ciki

- Wani mutum mai suna Martin Juuko ya wallafa matakin da ya dauka bayan da ya kama matarshi da wani gardi a shagon da ya bude mata

- Martin Juuko, ya bayyana yadda yayi wa Brendo tsirara tare da daureta sannan ya yi mata mugun duka

- Ya bude mata shagon siyar da kayan sawar maza ne, amma a rashin saninshi ta maida shagon ofishin karuwanci

Labarin wani fusataccen mutumi dan kasar Uganda wanda ya kama matarshi tana lalata da wani namiji a cikin shagon sayar da kayan sanyawa da ya bude mata, ya karade kafafen sada zumunta zamani.

A labarin da mutumin ya wallafa a Facebook, ya bayyana matakin da ya dauka a kan matarsa da ya kama da gardi a cikin shagon da ya bude mata. Ya yi mata tsirara tare da daureta sannan ya azabtar da ita ta hanyar dukanta.

Bayan nan, Martin Juuko ya yi bayanin yadda ya fatattaki Brenda Namuyomba a titi ta yadda makwabta suka dinga zundenta.

Kamar yadda Juuko ya sanar, ya bude mata shagon kayan sanyawar maza ne, amma bai san cewa tana kai samarinta don lalata a cikin shagon ba.

Juuko ya yi ikirarin cewa abun ya dade yana faruwa, amma dubunta ce ta cika ranar har ya kamata da daya daga cikin samarin nata.

Da kwarin guiwa kuma cike da isa Martin Juuko ya wallafa hotunan matarsa tare da tabbatar da duk kalma daya da ya wallafa da gaskiya.

KU KARANTA: Babu zancen son kai: Ni da Ali Nuhu mune babbar matsalar masana'antar Kannywood - Adam A Zango

Martin Juuko ya wallafa: “Kwastomomin shagon Praise ta Martin Juuko da ke rukunin shagunan MM, ina alhinin sanar da ku cewa na yanke hukuncin rufe shagon. Hakan ya biyo bayan kama matata Brenda Namuyomba da laifin mayar da shago ofishin karuwai bayan tana matsayin matata. Matata ta koma karuwa. Ta cire dan kamfan da na siya mata ga wani namijin.” Juuko ya wallafa.

“Tana samun komai a rayuwa. Ina bata daloli, na siya mata mota, ina kai ta kasashen ketare, na bata gida a Munyonyo, amma duk da haka take cin amanata. Abinda ya fi bata min rai shine, har da abokina take lalata,” Juuko ya kara.

Amma kuma, wasu daga cikin masu bibiyar shafinsa na Facebook sun bayyana cewa bai kyauta ba a matakin da ya dauka. Sun kwatanta hakan da kauyanci kuma sun bada shawara ga matar da ta kaishi kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel